TSARO A NAJERIYA: Buhari yayi duk abinda zai yi, hadin kan ‘yan Najeriya a ke bukata yanzu – Bashir Ahmad

Babban Hadimin shugaban kasa kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Bashir Ahmad, ya roki ƴan Najeriya su zo a haɗa hannu domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar.

Yankin Arewa musamman, Arewa maso Yamma da Gabas suna cikin raɗaɗin azabar hare-haren ƴan bindiga da mahara da kusan akullum sai an kashe mutane ko kuma an yi garkuwa da su.

Mutane a gida ba su samu natsuwa ba ballantana na kan hanyoyin kasar nan.

Sai dai kuma Bashir ya jinjina kokarin da shugaba Buhari ya ke yi wajen ganin ya kawo karshen waɗannan matsaloli da ake fama da su.

” Shugaba Buhari ya siyo manyan kayan aiki kama daga Motoci zuwa manyan jiragen sama na yaki wanda ake bugun kirji da su a duniya domin gamawa da waɗannan ‘ƴan bindigan da suka addabi mutane.

Bashir ya ƙara da yin kira ga ƴan Najeriya su musamman waɗanda suke yankin Arewa cewa su rika taimakawa jami’an tsaro da bayannan sirri da fallasa baki da suka shigo musu gari ko unguwanni da ba su san su ba ko kuma suke zargin su.

” ‘Yin haka zai taimaka matuka wajen ankarar da jami’an tsaro su zamo cikin shiri a koda yaushe domin tunkarar su da ragargazarsu a duk inda suke’”