SA-IN-SAR HANA JIRAGE ZIRGA-ZIRGA: Najeriya ta yi ramuwa kan Birtaniya, Canada da Saudiyya

Daga ranar 14 Ga Disamba ne Najeriya za ta hana jiragen sama da su ka fito daga Birtaniya, Canada da kuma Saudiyya sau filayen jiragen saman ƙasar nan.
Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika ne ya shaida haka ranar Lahadi a Legas, ya na mai ƙarin bayanin cewa hakan wata ramuwar gayya da Najeriya ta dauka, sakamakon hana jiragen da su ka ɗauki fasinja a Nijeriya shiga cikin ƙasashen uku, sakamakon fantsamar Omicron cikin Najeriya.
Sirika ya ce Gwamnatin Najeriya ta tsaya kan bakan ta cewa matsawar ƙasashen uku za su hana jiragen fasinjoji sauka ƙasashen su daga Najeriya, to kuwa ba su da hujjar barin jirage ɗauko fasinjoji daga ƙasashen su zuwa cikin ƙasar nan.
“Kun ga kamar Saudiyya ne, ta dakatar da mutane daga Najeriya shiga ƙasar. A ranar Lahadi na halarci taron da Kwamitin Daƙile Cutar Korona ya shirya.
“Sai mu ka cimma cewa bai yiwuwa mu bari ana shigo da fasinjoji daga ƙasashen da su ka hana fasinjoji daga Najeriya sauka filayen jiragen su. Har Ajantina ita ma za mu ɗauki mataki a kan ta.
“To idan sun hana fasinjoji daga Najeriya shiga ƙasashen su, me kuma jiragen su za su zo Najeriya su yi? Su wa jiragen za su ɗauka idan sun shigo?” Inji Sirika.
A ƙarshe dai Minista Sirika ya ba jama’a masu niyyar zuwa waɗannan ƙasashe haƙuri. Sannan kuma ya ce matakin da Najeriya ta ɗauka ta yi ne domin su amfanar kowa da kowa baki ɗaya.