ƘILU TA JA BAU: An warware naɗin basaraken da ya ragargaji gwamna

Lamiɗon Adamawa Muhammadu Barkinɗo ya warware naɗin ɗaya daga cikin masu rawanin jihar, saboda ya ce watandar motocin da Gwamna Ahmadu Fintiri ya yi wa sarakunan gargajiya a jihar, duk almubazzaranci ne.

Majalisar Masarautar Adamawa ta bayyana cewa ta warware naɗin da ta yi wa Umar Mustapha muƙamin Muƙaddas ɗin Adanawa.

Mustapha, wanda tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Adamawa ne a ƙarƙashin APC, ya fitar da sanarwar bayyana kyautar motocin a matsayin ɓarnar dukiya.

“Wannan watandar motocin da aka kashe har naira miliyan 200 aka sayo, aka raba wa sarakunan gargajiya, almubazzaranci ne. Ta yaya za a yi haka, alhali ga ɗimbin ‘yan fansho na mutuwa saboda yunwa.” Inji tsigaggen Muƙaddas ɗin.

Mustapha wanda ya fitar da sanarwar jim kaɗan bayan Gwamna Pintiri ya sanar cewa zai raba motocin, ya haɗu da fushin Lamiɗo, inda aka rubuta masa takardar warware naɗin sa, ta hannun Sakataren Masarauta, Khalil Kawu.

“Babban Basaraken Fombina kwata-kwata bai cancanci ci gaba da riƙe muƙamin sa ba, sakamakon caccakar da ya yi wa gwamna, don kawai zai raba wa sarakunan gargajiya motoci a jihar.

“Yadda ya saki linzamin bakin sa ya riƙa sheƙa wa gwamnati baƙaken kalamai, da kuma ragargazar sarautar gargajiya da ya yi, wadda shi ma a cikin ta ya ke, abin takaici ne matuƙa.” Haka sanarwar ta bayyana.

Lamiɗon Adamawa ya yi tir da yadda tsigaggen Muƙaddas ɗin ya kasa fahimtar abin alherin da gwamnati ta yi domin ƙara wa Sarautar Gargajiya martaba.

“Kyautar motocin da Gwamna Fintiri zai yi wa sarakunan gargajiya ta zo ne bayan an ɗauki dogon lokaci sarautar gargajiya ba ta ci moriyar komai daga gwamnati ba.

Don haka Lamiɗo ya ce bai ga dalilin da zai sa wannan kyauta ta zama abin yamaɗiɗi ba, a daidai lokacin da kamata ya yi a nuna godiya.

A ranar 1 Ga Disamba ne Gwamna Fintiri ya sanar cewa zai raba wa Sarakunan Adamawa kyautar motoci.