TSAKANIN TIWITA DA BUHARI: Karen Bana Maganin Zomon Bana

Bisa dukkan alamu ba cirewa ko dakatar da shafin tiwita ɗin Shugaba Buhari ne ya bata wa Gwamnatin Najeriya rai, har ta dakatar da Tiwita daga sahun kafofin soshiyal midiya a Najeriya ba.

Akwai alamun raini da nuna isa daga tiwita, idan kalaman shugaban kasa wanda yayi a matsayin sa na shugaban kasa kan ƴan kasar sa da ke ruruta wutar tada hankalun mutane da tarwatsa kasar, zai iya zama sanadiyyar kaiwa ga cire sakon Buhari a shafin, amma kuma a baya sun bar wasu rubuce rubucen da ke da muni da za su iya tada zaune tsaye a kasar a shafin su.

Sai dai kuma yayin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke ganin abin da Gwamnatin Najeriya ta yi daidai ne da ta dakatar da shafin Tiwata daga Najeriya, wasu miliyoyi da dama sun nuna haushin yadda cikin ƙanƙanen lokaci gwamnati za ta iya rufe shafukan tiwita, amma ba za ta iya gano inda ƴan bindiga su ke maƙale ba, ta hanyar amfani lambobin wayoyin hannun su, ko ta wanda su ka yi garkuwa da shi, domin a gano daidai wurin da su ke.

Sannan kuma da dama wasu na mamakin yadda shugabanni musamman na Arewa su ka fi maida hankali wajen batun dakatar da Tiwita, amma ba su cika ɗaukar kashe-kashen da ake yi a Arewa a matsayin babbar matsala kamar yadda su ka kalli Tiwita ba.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 88 a cikin Karamar Hukumar Danko Wasagu ta Jihar Kebbi, amma daga Gwamnatin Tarayya har ta Jihar Kebbi, babu wani ƙwaƙwaran matakin da su ka ɗauka. Ba a ma maida hankali kan kisan ba, kamar irin yadda aka maida hankali a kan abin da Tiwita ta yi wa Shugaba Buhari.

Kowa ya gani irin yadda Gwamnan Jihar Benuwai ke kwakwazo da rakaɗi ko da ƙudan-tsando aka kashe a jihar Benuwai. Amma sauran gwamnonin Arewa waɗanda kashe-kashe su ka buwaye su, ba su maida hankali sosai kan irin kashe-kashen da ake yi a jihohin su. Wasun su ma ba su cika so su ga ana bayyana adadin mutanen da aka kashe ba. Yanzu dai Tiwita ta koya wa mutane da yawa darasi. Sun gane cewa kalmomi goma kacal a Tiwita za su iya hana shugabanni barci. Amma kuma kisan takalawan ƙauye har mutum goma sau goma, ba zai sa gwamnti ta girgiza ba, kai ko gezau ma ba za ta yi ba.