NEJA BA LAFIYA: An arce da Madawakin Zungeru da matan sa biyu, mutum 18 sun nutse a ruwa wajen gudun tsira

Aƙalla mutum 20 aka bada labarin tabbatar da mutuwar su, lokacin da ‘yan bindiga su ka kai ƙazamin hari a garin Zungeru da kewaye a Jihar Neja.

An tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an kuma yi awon-gaba da Madawakin Zungeru, Al-Mustapha Mustapha, tare da matam sa biyu.

Mazauna garin sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa da farko an kashe mutum biyu, sai kuma wasu mutum 18 da aka tabbatar ruwan kogi ya halaka su, a ƙoƙarin gudun tsere wa ‘yan bindiga.

Zungeru gari ne da ke ƙarƙashin Karamar Hukumar Wushishi a Jihar Neja.

Majiyoyi da dama sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindiga sun ragargaji jama’a da dama a Zungeru da kewayen garin a ranar Juma’a.

“Da safe su ka fara rangadin kai hare-hare, tun ƙarfe 9 na safe, ido na ganin ido. Za su kai babura 70, kuma kowane da goyon ɗan bindiga a bayan babur ɗin banda mai ruƙawar shi ma da ta sa bindigar. A lokacin su ka fara dira garin Kudu, cikin Karamar Hukumar Rafi, inda ke kan iyaka da garin Zungeru.

“Daga can kuma sai su ka fara kai farmaki su na satar shanu, wayoyi da sauran dabbobi a Kutunku, Tashan Jarka, Tashan Jirgi, Babako, Utare, Agwa Buzu, har sai da su ka dangana Pakara.

“Daga Pakara kuma sai su ka juya, su ka koma ta ƙauyukan dai da su ka fara kuk-kutsawa kan su tsaye, duk a ranar Juma’a ɗin.” Inji wani mai suna Shehu.

“Daga nan kuma su ka yada zango, inda su ka yi sansani su ka zauna su ka huta a makarantar Firamare ta Kundu, kuma tare da dabbobin da su ka sata.

“Ƙarfe 6 na yamma na yi kuma, sai su ka datse babbar hanyar Minna zuwa Tegina har tsawon awa ɗaya, wato zuwa ƙarfe 7 na yamma.

Jama’a da dama sun ce an bindige mutane, kuma wasu sun faɗa Kogin Wushishi, a ƙoƙarin tsere wa ‘yan bindiga.

Hakimin Zungeru Salisu Abubakar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mutum biyu harbin harsashe ne ya kashe su, wasu 18 kuma ruwa ya ci su.

Kuma ‘yan bindigar sun arce da Madawakin Zungeru, Al-Mustapha Mustapha, tare da matan sa biyu. Sai dai kuma su a ranar Asabar wayewar garin Lahadi aka sace su.

“Cikin dare wajen ƙarfe 12:47 su ka dira gidan Madawakin Zungeru, Alhaji Mustapha. Kuma a lokacin bai dade da shiga gida ba, daga walimar auren wani maƙwaucin sa.” Haka wani mazaunin garin mai suna Kabiru Shehu ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Ya ce sunayen matan biyu da aka tafi da su, Aisha da Habiba.

Wani ɗan’uwan Madawaki ya ce har yanzu ‘yan bindigar ba su kira ba, ballantana a ji abin da su ke buƙata.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Neja bai ɗaga wayar sa ba, a lokacin da wakilin mu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin sa.