TAYA PANTAMI MURNA: Kungiyar Kiristoci CAN ta dakatar da shugaban kungiyar na jihar Gombe

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta dakatar da shugaban kungiyar reshen jihar Gombe saboda sakon taya ministan Sadarwa, Ali Pantami da ya yi bayan zama farfesa da Jami’ar Ower ta yi a makon jiya.

Bayan zama Farfesa da Pantami yayi daruruwan mutane yan Najeriya da waje sun rika aiko da sakon taya murna ga minista Pantami.

Shima shugaban kungiyar Kiristocin jihar Gombe Sunday Congo, ya aika da nashi sakon taya murnar, sai da kuma hakan ya bata wa uwar kungiyar ta kasa rai, nana da nan sai ta aika masa da sakon dsakatar dashi saboda sakon taya murnar da ya aika wa Pantami.

A cikin sakon, sun umarci Congo da ya mika takardu da duka wani abu na kungiyar dake karkashin ga mataimakin sa.

CAN ta ce Congo bai tuntube ta ba kafin ya aika da sakon taya murnar ga Pantami a dalilin haka kungiyar ta dakatar dashi.