Cin fuska ne da rainin wayau, cewa da Fani-Kayode yayi wai yana da hannu a komawa na APC – Gwamna Umahi

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya karyata kurin da tsohon ministan sufurin jiragen saman najeriya yayi wai na daga cikin wadanda suka karkato da ra’ayin sa ya koma jam’iyyar APC.

” Cewa da Fani-Kayode yayi wai yana da hannu a komawa na APC cin fuska ne da rainin wayau. Abokina ne na kud-da-kud amma ba shi da hannu a komawa na APC. Nine fa shugaban gwamnonin yanki Kudu Maso Gabas, a cewai sai wani Fani-Kayode ya yi min iso kafin na koma APC. Ai kun san wasan yara ne kawai.

Idan ba a manta Fani-Kayode ya bayyana komawarsa jam’iyyar APC ranar Alhamis a wata karamar kwarya-kwarya maraba da aka yi masa a fadar shugaban Kasa a Abuja.

Shugaban riko na jam’iyyar kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ne ya jagoranci tawagar yi wa shugaba Fani-Kayode iso zuwa wurin shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Bayan ganawar sa da Shugaba Buhari Fani-Kayode ya bayyana cewa lallai yayi wa Buhari Mummunar Fahimta ne a baya amma she mutumin kirki ne mai kishin kasa Najeriya.

” A baya na soki shugaba Buhari iya suka, ashe rashin zuwa kusa da shi ne da ban yi ba. A hankali a hankali da na kusance shi sai na gane cewa mutumin kirki ne mai kishin Najeriya. Hakan ya sa nima na dawo APC domin in taya shi gina kasar mu ta gado.