Jami’an tsaron NSCDC sun damke barayin dake fashi da na’urar POS a Kano

Rundunar tsaro na Sibul Difens NSCDC reshen jihar Kano ta kama wasu barayi biyu da suka addabi mutane da yin fashi da makami a karamar hukumar Gayawa Ungoggo.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Ibrahim Idris-Abdullahi ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a garin Kano.

Idris-Abdullahi ya ce ‘yan fashin mazauna kwatas din Danrimi, Rijiyar Lemo ne. An kama wadannan matasa a Gayawa, a lokacin da suke kokarinyi wa wata mata kwacen waya.

“An kama ‘yan fashin da wukake da na’uran POS.

Ya ce rundunar ta fara yin bincike akai domin a kamo abokan sana’ar su.

Idan ba a manta a makon da ya gabata ne PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi baje kolin wasu rikakkun barayi ne, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da ‘yan sara suka da suka addabi mutane.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ahmed Iliyasu ya ce rundunar ta kama duk wadannan batagarin a cikin kwanaki 20 da suka wuce.
Yace baya ga masu garkuwa da mutane da aka kamo, ankamo ‘yan daba dake farautar mutane suna kwace musu wayoyi, sannan da rikakkun barayi ‘yan fashi da makami da kuma yara masu satan kudaden mutane a yanar gizo, wato Yahoo-Yahoo.

An kwato komfutoci 4, ID card na sojoji da na ‘yan sanda, kayan sojoji, Gatari,takubba, barandami, fatefate, bindigogi kirar AK 47 da harsasai, kwalabe Kodin 125, dauri-daurin tabar wewe, wukake, baturan Sola, da wayoyin mutane da dama.