TATTAUNAWA DA SHUGABAN ƘASA: Buhari ba shi da abin da zai yi wa ‘yan Najeriya ya fitar da su daga ƙaƙa-ni-ka-yi – PDP

Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayi, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari Buhari ya kasa bayyana wani abin arzikin da ya yi wa ‘yan Najeriya.

Ayi na magana a kan tattaunawar da Buhari ya yi da gidan talbijin na Channels, wadda aka nuna a ranar Laraba da dare.

Daga cikin batutuwan da aka tattana da Buhari, har da rikicin makiyaya da manoma, batun neman ƙirƙiro ‘yan sanda na jihohi, Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe da zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ayu ya ce bayanin da Buhari ya yi a kan rikicin manoma da makiyaya ya nuna “Buhari a matsayin sa na shugaban ƙasa ba shi da wata sauran hikima ko dabarun kawo ƙarshen rikice-rikicen.”

A kan batun ‘yan sandan jihohi kuwa, Ayu ya ce za su yi amfani wajen cike gurabun wuraren da ba a iya tura ‘yan sandan tarayya aiki, saboda ƙarancin su.

Ayu ya ce kalaman Buhari kan matsalar tsaro sun nuna bai ma damu da irin zubar da jinin da ake yi a ƙasar nan ba.

Premium Times Hausa ta ruwaito Buhari na cewa ba kafa ‘yan sandan jihohi ne mafita daga ƙalubalen matsalar tsaro a ƙasar nan ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada rashin amincewar sa da kafa ‘yan sandan jihohi a ƙasar nan, a matsayin hanyar magance rashin tsaro a sassa daban-daban daban.

Ya yi wannan hasashen ne a lokacin da ake tattaunawa da shi a Gidan Talabijin na Channels, ranar Laraba da dare.

Gwamnonin ƙasar nan musamman a kudanci da tsakiyar Najeriya sun sha yin kiraye-kirayen neman kafa ‘yan sandan jihohi, a matsayin hanyar daƙile matsalar tsaro, musamman rikice-rikicen makiyaya da manoma da kuma hare-haren ‘yan bindiga.

Sai dai kuma Buhari ya ce idan doka ta bayar da dama jihohi su kafa ‘yan sandan su, to gwamnoni za su riƙa amfani da jami’an tsaron wajen yi wa ‘yan adawa ƙarfa-ƙarfa.

“Kafa ‘yan sandan jiha ba shi ne mafita ba. Babban misali shi ne abin da ke faruwa tsakanin ƙananan hukumomi da gwamnoni. Shin ƙananan hukumomi na samun abin da doka ta ce a riƙa ba su daga jihohi?

“A bar mutanen ƙananan hukumomi su faɗi gaskiya idan dangantar ƙananan hukumomi da jihohi ta na tafiya lafiya ƙalau.” Inji Buhari.

Da ya ke magana kan matsalar tsaro da neman mafita, Buhari ya ce tilas sai masu riƙe da ssrautun gargajiya sun tashi tsaye sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a yankunan karkara.

Sannan kuma ya ƙara jaddada bin hanyoyin zaman sasantawa tsakanin manoma da makiyaya domin magance rikice-rikicen da ke tsakanin su a faɗin ƙasar nan.

“Kada a raina muhimmiyar rawar da ta kamata sarakunan gargajiya su riƙa takawa ko yi wa ƙoƙarin su zagon-ƙasa wajen samar da zaman lafiya. Saboda sun san kowa a yankunan su. Sun kuma san gidan kowa.” Inji Buhari.