MULKIN NAJERIYA: Na yi bakin ƙoƙari na – Buhari

Duk da halin dagulewar matsalar tsaron da ake fama da ita a faɗin ƙasar nan, sai kuma halin ƙuncin rayuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi dai batun mulkin Najeriya ya yi bakin ƙoƙarin sa.

Buhari ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na NTA, wanda aka nuna a ranar Alhamis da dare.

An nuna wannan hira ce kwana ɗaya bayan nuna tattaunawar da Channels ta nuna, wadda gidan talbijin ɗin mai zaman kan sa ya yi da Buhari ɗin a ranar Laraba.

Shugaba Buhari ya ce shi dai ya san ya yi bakin ƙoƙarin sa. Saboda haka ya na fata da roƙon ‘yan Najeriya su riƙa tuna shi bayan ya sauka a matsayin wanda ya yi wa ƙara aiki tuƙuru bakin ƙoƙarin sa.

Buhari ya ce idan ya sauka zuwa zai yi ya huta kawai, bayan watanni 17 ɗin da suka rage masa.

“Abin da na ke jira na ji ‘yan Najeriya su na faɗi bayan na sauka, shi ne su riƙa cewa ‘ai mutumin nan ya yi bakin ƙoƙarin sa.

A tattauanawa da Channels ne Buhari ya ce matasa su daina tunanin yin ilmi don samun aikin gwamnati.

Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci matasan Najeriya cewa su yi watsi da tsohuwar al’adar yin ilmi don a samu aikin gwamnati.

Da ake tattaunawa da shi a Gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba da dare, Buhari ya ce yin ilmi ba wata hanya ba ce garanti da matashi zai ce sai ya samu aikin gwamnati.

“Ina fatan idan matasa je makarantu, idan sun yi ƙoƙari sun samu ilmi har sun samu digiri, to su daina tunanin sai sun yi aikin gwamnati.

“Ka daina dogaro da gwamnati ta ba ka aiki idan ka yi ilmi. Shi ilmi ana yin sa ne don mutum ya fayyace hanyoyin da zai warware wa kan ka matsalolin rayuwa. To ta nan ne za ka fi marar ilmi tunani.” Inji Buhari.

“Tsohuwar ɗabi’a ce tun ta zamanin mulkin Turawa, lokacin ne ake tunanin a yi ilmi don a samu aikin gwamnati, a mallaki mota.”

Najeriya na fama da matsalar yawan marasa aiki, kamar yadda ƙididdigar Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai (NBS) ta sha bayyanawa.

A ƙarshen shekarar 2020, NBS ta ce kashi 33.3 na ‘yan Najeriya masu ƙarfin iya yin aiki, ba su da aikin yi. Wato kusan matashi miliyan 23.3 kenan, ko kuma kashi 1 bisa 3 na su.

Cikin watan Yuni 2021, ne kuma Ministan Wasanni Sunday Dare ya ce za a buɗe rajistar neman aiki ga matasan Najeriya.

A wancan lokacin dai Ministan Harkokin Matasa da Wasanni, Sunday Dare, ya bayyana cewa zai shige a gaba domin tabbatar da cewa an bude rajistar matasa marasa aikin yi a kasar nan.

Wannan rajista da za a bude, Dare ya ce za ta saukake wa matasan kasar nan hanyoyin nema da samun aiki.

Ya ce tunanin bude rajistar ya biyo bayan kisan da aka yi wa wata matashiya a yayin da ta fita neman aiki a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a makon da ya gabata.

Yayin da ya ke mika ta’aziyya da jimamin rashin matashiyar mai suna Iniobang Umoren ga iyayen ta, Dare ya ce babban abin bakin ciki ne da tsananin tausayi kisan yarinyar, wadda wani mai suna Akpan ya yi.

Sannan kuma ya gode wa kawayen yarinyar da sauran jama’ar da su ka yi matukar kokarin fallasa wanda ya kashe ta.

Ministan Matasa Wasannni ya ce, “zan jagoranci hakilon ganin an bude Rajistar Tattara Sunayen Matasa Marasa Aiki, wadda za ta kasance a karkashin Rajistar Kididdiga ta Kasa.

A Najeriya dai ana fama da rashin aiki, inda cikin 2030 Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa, NBS ta ce rashin aikin yi ya kai kashi 33.3.

Lamarin ya kara tsanani ne saboda shi ma malejin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci sun kara cillawa sama.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da su ka fi fama da marasa aiki da zauna-gari-banza a duniya.