Yadda ‘yan bindiga suka babbake kauyuka biyar a jihar Zamfara

Akalla kauyuka biyar ne ‘yan bindiga suka cinna wa wuta a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar Zamfara.

Mazauna kauyukan da suka tsira da rayukansu sun samu mafaka a garin Anka.

Majiya da dama sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa har yanzu babu wanda ke da masaniyar yawan mutanen da aka kashe a wadannan kauyuka.

Wani lauya dake aiki da Kungiya mai zaman kanta a jihar Zamfara ya bayyana cewa ya ga mutane da dama da suka fito daga wadannan kauyuka da suka samu mafaka a hedikwatar Anka.

“Kafin na bar Gusau sai da na kirga mutum 500 da suka gudo daga kauyukan su inda a ciki akwai tsofaffi mata, ‘yan mata, mata masu shayarwa da kananan yara sannan rikicin ya fara a daren Laraba zuwa safiyan Alhamis.

Ya ce ya ga mutane wanda sarkin Ankan Zamfara ya aiki domin tallafa wa mutanen da suka gudo daga kauyukan su.

PREMIUM TIMES ta gano cewa Tungar Geza, Rafin Gero, Kurfar Danya, Kewaye da Tungar Na More na daga cikin kauyukan da ‘yan bindigan suka kona.

Bisa ga tattaunawan da wata majiya mai tushe ta yi da gidan jaridar VOA sashen Hausa wanda PREMIUM TIMES ta ji ya nuna cewa rikicin ya samo asaline tsakanin kungiyar ‘yan sa kai da ‘yan bindiga a kauyen Barikin Daji.

“Fadan ya fara tun a daren Talata. abin da ya fi firgita mu shine yadda suka cina wa kauyen Kurfar Danya wanda a sanin kowa wannan kauye ta fi samun tsaro a yankin.

“Daga nan sai suka koma kauyen Tungar Na More da Rafin Gero. Zuwa yanzu akwai gidajen da ke ci da wuta a kauyen Rafin Gero. Kauyukan Tungar Isa da Barayar Zaki na daga cikin kauyukan da ‘yan bindiga suka cina wa wuta.

Majiyan ya ce ba shi da masaniyar yawan mutanen da aka kashe a wadannan kauyuka sannan ya ce mafi yawan mutanen da suka samu mafaka a garin Anka na kan neman ‘yan uwansu.

Shugaban kungiyar matasa a karamar hukumar Bukkuyum Abubakar Gero ya ce rikicin ya fara ne a kauyen Kurfan Danya.

“Mun samu labarin cewa ‘yan bindigan sun afkawa kauyukan dake karamar hukumar Bukkuyum saboda arangama da suke yi da mutanen yankunan karamar hukumar, maharan sun zo da yawan gaske bisa babura da bindigogi.

“Daga kauyen Kurfan Danya sai suka shiga Ruwan jema nan ma sun kashe mutane da dama tare da kona abinci dake rumbuna.

“Zuwa yanzu ba a san yawan irin barnan da ‘yan bindiga suka yi a kauyen Ruwan Jema saboda har yanzu mazauna kauyen ba su koma kauyen ba.