TATTAKA HOTUNAN KWANKWASO: Yan siyasan Kano sun yi tir da abinda Ganduje ya yi

Tun bayan tattaka fostan tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi a wajen taron jam’iyyar APC a Kano ranar dimokradiya, yan siyasa sun soki wannan abu da kakkausar murya suna masu cewa, Ganduje ya wuce gona da iri.

Da yawa daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu har da wasu makusantan gwamnan kan al’amarin sun bayyana rashin jin dadin su sannan sun ce Ganduje ya wuce ya rika nuna karanta irin haka.

Wani tsohon kwamishinan Ganduje, Abdullahi Mu’azu wanda aka dakatar dashi a baya kan wasu kalamai marasa dadi da yayi game da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nuna karanta ne abinda gwamnan jihar yayi a matsayin sa na shugaba kuma dattijo.

” Ko dsai a banza shi Kwankwason ne kan gaba wajen lulawa da ganduje har yakai matsayin da yake yanzu. tare suke kaf a tsawon rayuwar siyasar su har ya kai ga darewa kujerar gwamnan jihar.

” Sannan kuma a matsayin sa na tsohon gwamna, tsohon Sanata, Tsonon mataimakin shugaban majalisa, Tsohon minista sannan a yanzu babu wani suna da ta ke da tasiri kamar sunan sa daga Kano a siyasar Najeriya, bai kamata Ganduje ya kankantar da kansa ba wajen aik abinda yayi a wajen taron ba.

Sai dai kuma wasu magoya bayan Gandujen sun ce basu ga wani abin tashin hankali akan abinda Ganduje yayi ba. Shi ma Kwankwason yaka tsakale shi saboda haka siyasa ce Ganduje yayi daidai.

Kwamishina yada Labarai na jihar Kano Mohammed Garba, ya bayyana cewa an yi wa bain da Ganduje yayi mummunar fahimta ne amma ba da gangar ya tattaka fostan Kwankwaso ba.

” Alokacin da gwamna Ganduje ya yi kokarin haurawa can saman ta matakala yayi wa dandazon ‘ya’yan jam’iyyar APC jawabi, sai kuma a gefen sa akwai wasu ‘yan Kwankwasiyya da suka yi turuwa wannan wuri suma za su canja sheka sai wasunsu suka rika jejjefa hotunan Kwankwasoa a kasa.

” Wurin taka matakala ne Ganduje ya rika tattaka wadannan fastoci da aka watsa a kasa hara akan matakalar ba wai da gangar an yi haka neda wata mnufa ba.

Jama’a da dama sun yi ta nuna rashin jin dadin su gane da abinda ya faru, inda suka ce Ido ba mudu bane amma ya san kima.