Gwamna Balan Buachi ya nada Aminu Gamawa sabon shugaban ma’aikata fadar gwamnatin jihar

Bayar cire tsohon shugaban gidan radiyon Tarayya, Ladan Salihu da a matsayin shugaban fadar gwamnatin jihar Bauchi da gwamnan jihar Bala Mohammed yayi a makon jiya, gwamnan ya nada Aminu Gamawa sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.

Idan ba a manta ba, gwamna Bala ya cire kafatanin kwamishinonin sa tare da sakataren gwamnatin jihar har da shugaban fadar gwamnatin jihar Ladan Salihu a wani garambawul da yayi wa yan siyasa da aka nada makamai a jihar.

An nada Gamawa kwamishinan Harkokin Kudi da tsare-tsare na jihar Bauchi a 2019, kuma shine shugaban kwamitin Korona na jihar.

Wannan nadi zai fara aiki ne nan take.