TASHIN HANKALI: Yadda cutar kansa ke kashe sama da mutum miliyan 10 kowace shekara a duniya – WHO

An bayyana cewa cutar kansa ta na kashe sama da mutum miliyan 10 kowace shekara a duniya.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta yi bayanin, tare da cewa mutum miliyan 2.7 cutar ke kashewa a cikin kasashen da ba su ɗauki kula da lafiya da muhimmanci ba, a ciki har da kasar nan.

Cutar kansa wadda ta fi yawa ita ce ta a kansa ta nono, wadda ta fi yawa ga mata.

Cikin 2020 cutar kansa ta nono ta kashe mutum 685,000 a duniya, daga cikin miliyan 2.3 da ta kama a nono, a duniya.

Cikin 2020 kansa ta kashe mutum 78,899 a Najeriya, waɗanda 34,200 maza, mata 44,699.

Babbar matsalar da masu fama da matsanancin ciwon kansa ke ciki, shi ne tsadar magani, domin gashi ya na kai ₦1,000,000.00.

Amma Shugaban Project Pink Blue, Runcie Chdebe, ya ce su na bada kulawa ga masu fama da cutar sama da 5,000 daga 2013 zuwa yanzu.

Ya ce likitocin da suka samu horo a 2018 za su iya kaiwa 44.

Watan da ya gabata aka ce cutar kansa ta kashe mutum 78,000 cikin shekarar 2020 a Najeriya.

Shugaban Cibiyar Bincike da Magance Cutar Kansa ta Kasa (NICRAT), Aliyu Usman, ya tabbatar da cewa cutar kansa ta kashe mutum 78,000 a ƙasar nan, cikin 2020.

Ya ce a shekarar, maza 34,200 ne su ka mutu sanadiyar kansa, mata kuma ta kashe har 44,699.

Shugaban na Hukumar Binciken Kansa ya ce kansa na iya ƙaruwa idan aka gano Indomin da ake ci Najeriya na da illa.

Cibiyar Bincike da Kula da Cutar Kansa ya Ƙasa (NICRAT), ta bayyana tsoron cewa idan har aka samu sinadarin ‘ethylene oxide’ mai haddasa kansa a cikin Indomi ɗin ake sarrafawa da sayarwa a Najeriya, to kuwa tabbas nan da da shekaru kaɗan masu zuwa za a samu ƙaruwar masu ɗauke da cutar ta ƙansa a Nijeriya.

Cibiyar binciken ta yi wannan hasashen ne biyo bayan samun samfurin sinadarin da ke haddasa cutar kan sa a Malaysia da Taiwan.

Sai sai kuma Indofoods kamfanin da ke yin Indomi ya ƙaryata zargin samun sinadarin da ke haddasa kansa a cikin indomi.

Duk da cewa Indomi ɗin da ake ci a Najeriya duk a ƙasar nan ake yin ta, NAFDAC ta ce ta fara bincike domin tabbatar da cewa dukkan wadda ake haɗawa kuma ake ci a ƙasar nan ba ta da wata illa.

Ƙananan Yara Sun Fi Shiga Barazana:

A wata sanarwa da Babban Daraktan NICRAT, Cibiyar Binciken Kansa ya fitar, Usman Aliyu ya ce an gano cewa sinadarin ethylene oxide’ na da gubar da ke yi wa ɗan Adam mummunar illa, idan ya ci abinci mai ɗauke da ɓurɓushin sinadarin.

Aliyu ya ce idan har aka samu sinadarin a Indomi ɗin da ake ci a Najeriya.

Ya ce saboda ƙananan yara ne su ka fi cin Indomi a Najeriya.

NAFDAC ta ce binciken gwajin ta ba kan Indomi kaɗai zai tsaya ba, za ta faɗaɗa har sauran dangogin ta, ko irin ta waɗanda sunaye ne su ka bambanta su.

NICRAT, cibiya ce ta Binciken Cutar Kansa, wadda aka kafa cikin 2017 domin bincike, gwaji, warkaswa da hana kamuwa da cutar.

Yadda Kansa Ke Mummunan Kisa A Najeriya – Aliyu:

Aliyu ya ce a shekarar 2020 kaɗai, kansa ta kashe mutum 78,000 a Najeriya.

Ya ce a cikin waɗanda ta kashe ɗin, 34,200 maza ne, mata kuwa 44,699.

A Najeriya dai an fi cin indomi samfurin ‘instant noodles’, wadda a cikin ƙasar nan ake yin ta.

Ƙididdiga daga Kungiyar Masu Indomie Noodles’ na Duniya, Reshen Najeriya, ya ce indomi ce abincin da ya fi zama karɓuwa ga jama’a.

Sannan kuma Najeriya ce ƙasa ta 11 a duniya, a jerin masu cin indomi.