KADUNA: Mamman-Legas, Shagali, Bello sun tsinduma cikin sunayen Kwamishinonin Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya aika da sunayen wadanda zai nada Kwamishinonin sa zuwa majalisar Dokokin jihar.
Duk da cewa babu wani sabon suna a cikin jerin sunayen da ba ariga an tsammane shi ba, ana sa ran nan ba daddewa ba majalisa za ta fara tantance su domin gwamnati ta fara aiki gadan gadan.
1 – Umma Kaltume Ahmed
2 – Mukhtar Ahmed
3 – Arch. (Dr.) Ibrahim Hamza
4 – Sule Shu’aibu
5 – Auwal Musa Shugaba
6 – Shizzer Nasara Joy Bada
7 – Salisu Rabi Hajia
8 – Patience Fakai
9 – Abubakar Buba
10 – Professor Muhammad Sani Bello
11 – Professor Benjamin Kumai Gugong
12 – Hon. Saddiq Mamman Lagos
13 – Murtala Mohammad Dabo
14 – Abdullahi Aminu Shagali
Sabbin Nade-nade
A ci gaba da ragargaza sabbin hadimai da shugabannin ma’aiktu da gwamnan Kaduna ya ke yi, a ranar Talata ya sanar da nadin sabbin nade-nade a jihar.
Kakakin fadar gwamnatin Jihar, Hohammed Shehu ya sanar da haka a sanarwa a garin Kaduna.
Wadanda aka nada sun hada da:
1. Mohammad Sada Jalal – Darektan ma’aikatan Sufiyo da tsaretare na jihar (Kaduna Geographic Information Service (KADGIS)
2. Jerry Adams – Shugaban Hukumar tara haraji na jihar Kaduna (KADIRS)
3. Adamu Magaji – Darekta Janar na Ma’aikatar (Kaduna State Facility Management Agency) (KADFAMA)
4. Adamu Samaila – Babban mai ba da shawara kan harkoki ma’aikata da da kungiyoyin Kwadago
5. Amina Sani Bello – Mai taimaka wa gwamna na musamman kan harkokin Dalibai
6. Salisu Ibrahim Garba – Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa
7. Larai Sylvia Ishaku – Mai ba da shawara na musamman (Social Investment Programme)
8. Clement Shekogaza Wasah – Mai ba da shawara na musamman, (Community Engagement)
9. Waziri Garba – Mai ba da shawara na musamman, Harkokin Yau Da Kullum.
Har yanzu a na sauraren sunayen Kwamishinonin da gwamna uab Sani zai nada.