TASHIN HANKALI: Saboda lalacewa yanzu, har Nas-Nas na fede mutum asibitoci

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Enugu Celestine Ugwuoke ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta mike tsaye wajen tsara hanyoyin da za su taimaka wajen kawar da baragurbin ma’aikatan lafiya a jihar.

Ugwuoke ya yi wannan kira ne domin jawo hankalin gwamnati kan yadda wasu baragurbin jami’an lafiya ke kashe mutane saboda rashin kwarewar su a aiki.

Ya ce a jihar Enugu nas-nas na yi wa mutane fida wanda a bisa tsari yin fida baya cikin aikin da ya kamata suna yi.

“ Masu manyan shagunan siyar da magani wanda aka fi sanin su da ‘chemist’ a dan cikin shagon su na yi wa mutane Karin ruwa.

“ Dalilin haka mutane ke yi mutane da dama sun rasa rayukansu a jihar.

Ugwuoke ya ce kungiyar ta dauki wasu matakai domin dakatar da yin irin haka a fadin jihar.

“Ina kira ga gwamnati da ta taimaka wajen daukan matakan da za su hana baragurbin ma’aikata lafiya wajen ci gaba da kisar mutane a jihar.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta inganta albashi, alwaus da wurin aikin ma’aikatan lafiya cewa yin haka zai taimaka wajen hana yawan ficewar kwararrun jami’an lafiya daga kasar nan zuwa kasashen waje.