Kungiyar Ma’aikatan kiwon lafiya JOHESU ta fara yajin aikin gamagari

Gamayyar kungiyar Kiwon tafiya ta Kasa ta fara yajin aikin daga yau Alhamis 25 ga Mayu.

Mataimakin shugaban kungiyar JOHESU na kasa, Obinna Ogbonna ya sanar da bayan taron kungiyar ranar Alhamis a Abuja.

Ogbonna ya bada dalilin fara yajin aikin kan kin waiwayan su da gwamnati ta yi na daidaita albashin ma’aikatan dake karkashin kungiyar daidai da sauran ma’aikatan lafiya bisa tsarin albashi na (CONHESS).

” A dalilin kin amincewa da biya mana bukatun mu, ciki har da daidaita albashin ma’aikata da ke karkashin kungiyar JOHESU da kuma sauran korafe korafen mu dake gaban ma’aikatan lafiya ta kasa ya sa dole a wannan karan mu hakura mu fara yajin aikin har sai gwamnati ta biya mana bukatu.