Kungiyar Tarayyar Turai Ta Ci Tarar Facebook $1.3 Biliyan
Kungiyar Tarayyar Turai ta ci tarar Meta, babban kamfanin da ya mallaki Facebook, dala biliyan 1.3 tare da umartarsa da ya daina mika bayanan masu amfani da shafin zuwa Amurka nan da watan Oktoba.