Ku daina la’antar shugabanni saboda wahalar rayuwa, Sanusi ga ƴan Najeriya

Tsohon Sarkin Kano kuma jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sunusi na II, ya shawarci ƴan Najeriya da su daina zagin shugabanni da la’antar su kan wahalhalun da ake fuskanta a ƙasar nan.
Ya yi wannan ƙiran ne yayin da yake ganawa da mabiya Ɗariƙar Tijjaniyya daga jihohi bakwai na shiyyar Arewa maso Yamma a ranar Talata a jihar Sakkwato, a cewar wata sanarwa.
Jaridar Punch ta ruwaito tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya ba da shawarar cewa maimakon tsine wa shugabanni, ya kamata ƴan Najeriya da mabiya Tijjaniyya su kasance masu addu’a, yayi fatan cewa Najeriya za ta gyaru.

Ya kuma yi gargaɗi game da rashin biyayya ga hukumomin da aka kafa bisa doka, yana mai nuni da cewa yakamata a yi komai bisa doka.
An nakalto Sanusi yana cewa, “Abin da ake buƙata a gare mu yanzu shine haƙuri, addu’o’i masu ƙarfi kuma dole ne mu tashi tsaye don ganin abubuwa sun inganta a namu hanyar ta halal.
“Dole ne mu guji cin zarafi ko la’antar shugabanninmu saboda wahala da aka shiga domin Manzon Allah ya hanemu da yin hakan.
“Bai kuma kamata mu saka kanmu cikin gurbatattu da sauran miyagun ayyuka ba saboda addininmu ya yi hani da hakan.
“Dole ne mu canza halayen mu kuma mu kasance masu himma ga zaman lafiya da ci gaban al’ummomin mu.”
Tsohon Sarkin ya kuma buƙaci membobin ɗarikar da su tsunduma cikin siyasa a yayin da zaben 2023 ke gabatowa.
Sanusi ya ƙara da cewa “Lokacin da ƴan siyasa suka tunkare ku yayin zabe, ku buƙaci a gina muku makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya da sauran su,” in ji Sanusi.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 22, 2021 6:02 AM