TABARBAREWAR TSARO: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 78 a makon jiya a Najeriya

Akalla mutum 78 ne ‘yan bindiga suka kashe a makon jiya a Najeriya, daga ranar 1 zuwa 5 ga Mayu.
Daga cikin mutum 78 din da ‘yan bindigan suka kashe akwai sojoji biyu da ‘yan sanda uku sannan da mutanen gari.
‘Yan kungiyar IPOB sun fille kan sojoji biyu sannan ‘yan bindiga sun kashe mutum 56 a jihar Zamfara.
‘Yan bindigan sun kashe mutum 78 a yankin Kudu maso Gabas, Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Kudu maso Gabas
A ranar Lahadi ‘yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Imo.
‘Yan bindigan sun harbe wani soja maisuna A. M. Linus da matarsa wacce ita ma soja ce ta hanyar fille kawunan su da takubi.
Hotuna da bidiyon gawarwakin sojojin ya kareda sada zumunta a yanar gizo.
A jihar ne ‘yan bindiga suka kashe sufritanda din ‘yan sanda Ukam Efut yayin a lokacin da yake aikin sintiri a kauyen Agwa dake karamar hukumar Oguta.
Rundunar ‘yan sanda sun kashe ‘yan IPOB biyu a kauyen Agwa dake karamar hukumar Oguta.
Hakan ya auku ne yayin da ‘yan bindigan suka fito daga daji suka buda wa ‘yan sanda wuta inda har suka kashe dan sanda daya.
A jihar Ebonyi wasu matasa sun kashe wata budurwa mai suna Ugochukwu Nworie mai shekaru 26 bayan sun yi mata fyade.
Matasan sun aikata wannan mummunar abu a Otel din ‘Hope-in’ dake layin Nine Ngbowo, Abakaliki ranar Litinin da ya gabata.