SUNAYE: Sabbin ministocin da Buhari ya aika sunayen su majalisar Dattawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da sunayen sabbin ministoci 7 da ya nada zuwa Majalisar Dattawa domin a amince da su.
Idan ba a manta ba, shugaba Buhari ya umarci duk ministocin da suka sayi fom ɗin takarar shugaban kasa su ajiye aikin su, wanda kuma.dukkan su sun yi.
Ya yi alkawarin zai gaggauta musanya su da sabbin ministoci.
Sunayen da Buhari ya aika majalisa sun haɗa da Henry Ikechukwu – Abia State, Umana Umana – Akwa Ibom State, Ekuma Joseph – Ebonyi State da Goodluck Obia – Imo State.
Sauran sun haɗa da Umar Yakub – Kano state, Ademola Adegorioye – Ondo State da Odo Udi – Rivers State.