KIWON LAFIYA: Me cece cutar Monkey pox, alamun kamuwa da cutar, hanyoyin da za a kiyaye don gujewa kamuwa da cutar

Cutar ‘Monkey Pox’ cuta ce da take kama fatar mutum inda zaka ga mai dauke da cutar na fama da wasu irin manya-manyan kuraje kamar kazuwa.
Cutar ya fara bullowa a Nahiyar Afrika a shekarar 1970 sannan ya bayyana a shekaran 1978 a Najeriya.
Tun daga wancan lokaci cutar bata sake bayyana ba sai a shekarar 2017 a jihar Bayelsa.
Yadda Monkey Pox ke shiga cikin jikin dan Adam
Rahotanni sun nuna cewa namun daji kamar su birai da beraye dake shawagi a gidajen mutane na daga cikin ababen dake kawo cutar ‘Monkey Pox’.
Sannan kuma cutar na yaduwa idan ana yawan zama kusa da wadanda suka kamu da cutar.
Ana kuma iya kamuwa da cutar idan aka yi jima’i da wanda ya ke ɗauke da cutar.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce kwayar cutar ‘Monkey Pox’ yakan dauki tsawon kwanaki 6 zuwa 16 kafin ya fara nunawa a jikin mutum.
Alamu dake nuna an kamu da cutar monkey pox.
1. Zazzabi.
2. Yawan jin gajiya a jiki.
3. Ciwon jiki musamman baya.
5. Kumburin jiki musamman idan cutar ta fara nunawa.
6. Bayyanan kuraje a jiki
Hanyoyin da za a bi don gujewa kamuwa daga cutar
1. A daina cin naman dabbobin daji kamar su biri, burgu da bera.
2. A hana dabbobi yawo musamman wadanda ke kiwon su domin kada su fita su dauko cutar daga jikin dabbobin da suke dauke da cutar kuma a killace dabbobin da suka kamu da cutar saboda hana yaduwar ta.
3. Mutane su nisanta kansu daga dabbobi musamman daga kashin su da kuma jikinsu.
4. Kada a zauna daki daya da mutanen da suka kamu da cutar.
5. A yi amfani da safan hannu wajen kula da mutanen da suka kamu da cutar musamman ma’aikatan asibiti sannan idan aka ziyarci wanda ke dauke da cutar a tabbatar an wanke hannaye da ruwa da sabulu bayan an fito.
6. A tabbatar cewa a kowani lokaci ana tsaftace muhalli.
7. Sumbatar mai dauke da cutar kan iya sa a kamu.
8. A rage shan hannu ko ta yaya sannan a yi amfani da man tsaftace hannu.
9. Hukumar dakile yaduwar cututtuka dake kasar Amurka CDC ta ce Kaurace wa juna, mutum zai iya yi wa kansa wasa har sai ya samu gamsuwa da rufe bangaren jikin da kurarrajin cutar suka feso kafin a sadu.
Yaduwar cutar monkey pox a Najeriya
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 141 da ake zargin sun kamu da cutar Monkey pox a jihohi 13 a kasar nan.
A baya adadin yawan da ake zargin sun kamu da cutar sun kai mutum 110 a Najeriya.
Zuwa yanzu cutar ta yaɗu zuwa kasashen da basu da tarihin an taɓa samun bullar cutar.
NCDC ta ce daga cikin mutum 141 din da ake zargin sun kamu da cutar sakamakon gwaji ya nuna cewa mutum 36 ne suka kamu da cutar a jihohi 14 da Abuja daga ranar 1 ga Janairu zuwa 12 ga Yuni 2022.
Jihohinsu hada da Legas-7, Adamawa- 5, Delta- 3, River -3, Cross River -2, Kano -2, Bayelsa -2, Edo -2, Imo -2, Filato-2, Nasarawa -1, Niger -1, Oyo -1, Ondo -1 da Abuja-2.
A shekaran 2022 mutum daya mai shekara 40 dake fama da wani cuta baya ga Monkey Pox ya mutu.
Daga watan Satumbar 2017 zuwa ranar 12 ga Yuni 2022 an samu mutum 653 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 33.
Daga cikin mutum 262 din da aka gano an samu tabbacin cewa kashi 40.1% sun kamu da cutar a jihohi 23.
Jihohin sun hada da Rivers -55, Bayelsa -45, Legas – 37, Delta -32, Cross River -16, Edo -12, Imo -10, Akwa Ibom -7, Oyo -7, Filato -5, Adamawa -5, Enugu -4, Abia -3, Nasarawa -3, Benue -2, Anambra -2, Ekiti -2, Kano -2, Niger -2, Ebonyi -1, Ogun -1, Ondo -1 da Abuja-8.
Mutum 9 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar a jihohi shida daga Satumba 2017 zuwa 12 ga Yuni 2022.
Jihohin sun hada da Legos- 3, Edo -2, Imo -1, Cross River -1, Abuja -1 da Rivers -1.
Yaduwar cutar monkey pox a wasu kasashen duniya
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa mutum 257 ne suka kamu da cutar a kasashen dake karkashin ta.
WHO ta ce an gano wadannan mutane daga ranar 13 zuwa 26 ga watan Mayu.
Daga cikin kasashen kasar UK ta fi fama da yaduwar cutar inda mutum 106 suka kamu, Portugal – 49 da Canada – 26.