SSS sun gargadi masu furta munanan kalaman da ka iya haddasa fitina su daina

Hukumar ‘Yan Sandan Leken Asiri ta Kasa (SSS ko DSS) ta fitar da sanarwar kakkausan gargadi ga musamman manyan mutane masu furta munanan kalaman da ka iya haddada tarzoma da dagulewar zaman lafiya a kasar nan.

Sanarwar da Kakakin SSS, Peter Afunanya ya fitar s ranar Litinin, ta zo ne bayan babban fasto Ejike Mbaka ya nemi a tsige Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari, saboda abin da ya kira lusarancin Buhari wajen kasa magance matsalar tsaro a kasar nan.

Sannan kuma sanarwar ta zo kwanaki bayan da SSS su ka tsare Usman Bugaje tsawon sa’o’i takwas su na yi masa tambayoyi, bayan ya caccaki Shugaba Buhari a wata hira da aka yi da shi a Gidan Talbijin na AIT.

“Wannan gargadi ya na magana ne musamman ga masu kiran jama’a su fito su nuna wa gwamnati fushin su, ko masu kiran a canja gwamnati da karfin tsiya, domin su na yi da nufi da niyyar tarwatsa kasar nan.”

Sai dai kuma har yau SSS ba su gayyaci gogarman ‘yan iskan yankin Kudu maso Yamma, Sunday Igboho ba, wanda ya rika jan zugar dandazon matasa ana banka wa rugagen Fulani wuta.

SSS sun ce kowa na da ‘yancin fadin ra’ayin sa, amma doka ta haramta furta kalaman da za su iya haddasa tashin hankali.

Yayin da Fadar Shugaban Kasa ta ce Mbaka ya ragargaji Buhari saboda haushin ya nemi kwangila bai samu ba, ita ma APC ta ragargaji babban fasto Mbaka don ya ce Buhari ya gaza, ya sauka ko a tsige shi.

Jam’iyyar APC ta ragargaji babban limamin Kirista, Ejike Mbaka, wanda bayan ya shafe shekaru ya na goyon bayan Shugaba Muhamamdu Buhari, a wannan karon kuma ya kware masa baya, ya ce ba ya iya samar da tsaro a Najeriya, don haka ya sauka kawai.

APC ta ce kalaman da Mbaka ya yi amfani da su sun yi tsaurin da za su iya haddasa tarzoma a kassr nan.

Kakakin APC Yekini Nabena, ya yi barazanar kai karar Mbaka a Babban Cocin Katolika, idan ya ci gaba gaba da kinkimo danyar magana ya na dankara wa Gwamnatin Tarayya.

Mbaka wanda shi ne Shugaban Cocin Adoration Ministry da ke Enugu, kwanan nan ya yi kira ga Majalisar Tarayya ta tsige Shugaba Buhari idan ya ki sauka saboda ya kasa samar da tsaro a kasar nan.

Mbaka dai ya yi wannan furuci a cocin sa, inda ya yi kira ga fadar shugaban Kasa ts gaggauta kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

Yekini Nabena ya ce kamata ya yi Mbaka ya maida hankalin da wajen ibada a cocin sa, maimakon ya rika tsoma baki cikin siyasa, wadda babu abin da ya sani a cikin ta ko a wajen ta.

Ya kalubalanci Mbaka ya yi amfani fa cocin sa wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya a kasar nan.

Ya nemi Mbaka ya yi koyi da Yesu Almasihu, wanda ya ce ya bi hukuma sau da kafa a rayuwar sa, har zakka ya rika biya.

Ya nemi Mbaka ya maida hankali a coci, ya kyale ‘yan siyasa su yi siyasar su.