An kashe mutum 97, an yi garkuwa da wasu 58 cikin makon jiya

Yayin da aka kashe mutum 239 aka sace wasu 44 cikin makon shekaranjiya a fadin kasar nan, kididdigar rahotannin makon jiya kuma ta tabbatar da kisan mutum 97 tare da yin garkuwa da wadansu mutum 58 a fadin kasar nan.

Adadin wadanda aka kashe da na wadanda aka sacen dai duk wadanda kafafen yada labarai su ka buga ne kadai. Akwai da dama wadanda aka kashe ko aka yi garkuwa da su, amma jaridu ba su buga ba, saboda rashin samun rahotannin.

Rashin tsaro ya kara rincabewa tun a farkon makon da ya wuce, bayan da Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja ya bayyana cewa Boko Haram sun kafa tuta a kauyen Kaure, cikin Karamar Hukumar Shiroro, har sun kwace matan auren mazauna kauyen sun yi watanda a tsakanin su.

Shi ma Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutum 70 cikin makonni biyu a Karamar Hukumar Makurdi.

A Jihar Ribas and kashe jami’an ‘yan sanda takwas, a wani hari da masu dauke da bindigogi su ka kai masu.

An yi garkuwa da mutum 35 a kauyukan Chiri, Gini da Fuka, cikin Karamar Hukumar Shiroro da Karamar Hukumar Munya da ke Jihar Neja.

A jihar Anambra an kashe mutum takwas a harin da hasalallun ‘yan iskan gari su ka kai wa al’ummar Awkuzo da ke Karamar Hukumar Oyi.

PREMIUM TIMES HAUSA ta fassara makon shekaranjiya da: Makon Rubdugun Kisan Talakawa”, inda ta buga labarin an kashe mutum 239, an sace mutum 44 a makon jiya.

Halin da talakawa su ka shiga a makon da ya gabata a sassa daban-daban na kasar nan, ya kara nuna ci gaba da kasawar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen kare ratuka da dukiyoyin jama’ar kasar nan.

Munin kashe-kashen makon da ya gabata ne ya kai ga Wole Soyinka fitowa ya bayyana cewa Najeriya fa ta rufka yanayin yakin ‘katilan-makatulan’, amma gwamnati ta kauda kai ba ta yarda yaki ne ake yi gaba-gadi ba.

Cikin makon da ya gabata kididdigar labarai ta bayyana cewa an kashe akasarin talakawa 239 kuma aka yi garkuwa da mutum 44 duk a cikin mako daya.

Yayin da a Jihar Zamfara aka kashe mutanen karkara sama da 90 a hare-hare daban-daban a Magami da kewaye, cikin Karamar Hukumar Gusau, a Jihar Yobe Boko Haram sun yi dirar mikiya a Geidam, garin haihuwar sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali.

A jihar Oyo kuma ‘yan bindiga ne su ka tare hanya su ka yi gaskuwa da dukkan fasinjoji 18 da ke cikin wata motar haya.

Matsalar tsaro ta kai ga an kai hari da rokoki a gidan Gwamnan Imo Hope Uzodinma, kamar yadda a baya aka taba kai wa jerin gwanon motocin Samuel Ortom na Benuwai hari a cikin daji.

Irin haka ta faru da Gwamna Babagana Zulum na Barno, ba sau daya ba an kai masa hari.

A jihar Katsina ma mahara sun yi garkuwa da mata su 20 da su ka halarci bikin radin suna.

Haka a jihar Kaduna ‘yan bindiga sun saci daliban jami’ar Greenfield University, kuma su ka kashe uku daga cikin su.

Matsalar tsaron da ke ci gaba da faruwa ta nuna canja manyan hafsoshin tsaro da kuma canja Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, duk an ki cin biri ne, an ci dila.