Sojojin Najeriya sun hana Boko Haram arcewa da matafiya, sun ceto wasu mutum 17 a gumurzun Barno

Zaratan Sojojin Daƙile Boko Haram na Sashe na 1 ‘Yan ‘Operation Haɗin Kai’, sun karya lagon Boko Haram, waɗanda su ka tare kan titin Maiduguri zuwa Damaturu da nufin arcewa da matafiyan da su ka tare a kan hanyar.
Daraktan Yaɗa Labarai Onyema Nwachukwu ya bayyana haka a ranar Talata a Abuja.
Ya ce ‘yan ta’adda sun datse hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, inda su ka yi ƙoƙarin shiga garin Auno da ƙarfin tsiya, amma sojojin Najeriya su ka tare su aka yi karon-batta.
“An sake yin taho-mu-game ɗin karon-batta yayin da sojojin Garison na 7 su da Bataliya ta 212 su ka yi nasarar ceto wasu matafiya waɗanda aka kama a Kontori, kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.”
Ya ce tuni waɗanda aka ceto ɗin an damƙa su ga jami’an da kula da su, ya shafa, wato RRS.”
“Idan za ku iya tunawa, to a lokacin gaggawar zuwa yin wannan artabu ne wasu sojoji su ka yi hatsari a mota wurin gudun kai ɗaukin gaggawa.
“Tuni Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya jinjina wa sojojin bayan sun saka wa zaratan Boko Haram dukan tsiya.
“Yahaya ya kuma nuna aniyar sa ta ƙara samar wa dakaru makamai na zamani tare da ba su kyakkyawar kulawa.