Majalisar Dattawa ta ki amincewa da naɗin Lauretta Onochie a matsayin kwamishina a hukumar zaɓe

Kwamitin Zaɓe na majalisar Dattawa, Ƙarƙashin shugabancin sanata Kabiru Gaya, ta mika wa majalisar rahoton tantance zaɓin shugaba Buhari wanda ya aika wa majalisar domin a tantanceta ta zama kwamishina a hukumar zaɓe.

Sai dai kuma rahoton sakamakon tantancewar da aka mika a zauren majalisar ranar Talata, ya nuna cewa kwamitin bata amince a nada ta kwamishina a hukumar zaɓe ba.

Hujjar da Sanata Kabiru Gaya ya bada a lokacin da ya ke karanta matsayar da kwamitin ya ɗauka ya ce Lauretta Onochie ƴar asalin jihar Delta ce kuma akwai wanda ke wakiltar jihar Delta a Hukumar, saboda haka kwamitin ba ta amince da naɗinbta kwamishina a hukumar zaɓe, wanda hakan shine matsayar majalisa.

Dama kuma tun bayan naɗin Lauretta Onochie, kasa ta ɗauki zafi, ana ta yin fashin baki akan wannan naɗi da shugaba Buhari yayi mata.

Da dama mutane na ganin a matsayin ta na mai taimakawa shugaba Buhari kan sabbin kafafen yaɗa labarai na bai kamata kuma a naɗata kwamishina a hukumar zaɓe ba.

Hakan zai zama kamar rufe gida ne da ɓarawo.

Tsohon shugaban hukumar Zaɓe, Attahiru Jeha shima ya soki naɗin Lauretta Onochie, yana mai cewa shima yana goyon bayan kada a naɗa ta a hukumar INEC ɗin.