Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 31, sun kama 70 a yankin Arewa maso Gabas

Hedikwatar Hukumar tsaron ƙasa DHQ ta bayyana cewa dakarun rundunar ‘Operation Hadin Kai OPHK sun kashe Boko Haram/ISWAP 31 sannan sun kama ƴan ta’adda 70.
Darektan yada labarai na hukumar tsaron Najeriya manjo-janar Musa Danmadami ya sanar da haka a Abuja yayin da yake bayyanin aiyukan da dakarun rundunar suka yi cikin makonni biyu da suka gabata.
Danmadami ya ce mutum 60 cikin 70 din da aka kama masu yi wa ‘yan ta’adda hidima ne, wato ƴan aike, da safarar kwayoyi da suke musu da kuma abubuwan da ba a rasa ba.
Ya ce dakarun sun ceto mutum biyu da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su. Sannan ‘yan ta’adda 366 da iyalen su sun mika wuya.
Danmadami ya ce a ranar 11 ga Oktoba dakaru sun kashe ‘yan ta’adda 18 da suka yi wa jami’an tsaron zobe a Bama da Ngala.
Jami’an tsaron sun kwace makamai da dama da ‘yan ta’addan suka gudu suka bari.
Ya ce dakarun sun kashe ‘yan ta’adda 17 sannan daga cikin makaman da suka kama akwai bindiga kirar GPMG ɗaya, Ak-47 guda biyar, bindiga kirar M21 guda daya da babura 11.
Sauran kayan da aka kama sun hada da AK 47 guda 14, GPMG biyu, M21 guda daya, bom artillery milimita 125, harsasai milimita 7.62 guda 40, bindiga kira Dane gun guda shida, bindiga na hannu guda daya, mota daya, wayar salula 4, kekuna biyar da babura 11.
“Dakarun sun kama buhunan wake 64, buhunna biyar na masara, kullin wiwi, magunguna, daurin kayan sakawa sabbi, kaji 46, tsabar kudi Naira 250,000 da dai sauran kaya.
Jami’an tsaro sun kama ma’aikatan boge na hukumar NIMC
Danmadami ya ce a ranar 13 ga Oktoba sojoji da hadin gwiwar ‘yan sanda da jami’an hukumar kula da shige ta kasa sun kama wasu ma’aikatan NIMC na boge guda biyu.
Ya ce jami’an tsaron sun kama wadannan mutane yayin da suke yi wa wadanda ba ‘yan Najeriya rajista a cikin sansanin ‘yan gudun hijiran Gagamari IDP a matsayin ‘yan Najeriya a Jamhuriyar Nijar.