RIGIMAR MASU FUKAFUKI: Dalilin da ya sa mu ke adawa da kafa Nigeria Air -Masu harkokin jiragen cikin gida

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tilas ne Nigeria Air ya fara zirga-zirga nan da watan Disamba, wani rikici ta kunno kai, inda masu harkokin zirga-zirgar jirage na cikin gida, wato ‘Airline Operators of Nigeria (AON), su ka nuna rashin goyon bayan kafa kamfanin.
Kungiyar ta bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai ta Ƙasa mai kula da harkokin sufurin jiragen sama a ranar Alhamis, kuma ta shaida cewa yadda idon Gwamnatin Tarayya ya rufe har ta amince kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama na Ethiopian Airlines ya mallaki kashi 49 na hannun jarin Nigeria Air, tsari ne da zai gurgunta jiragen saman cikin gida.
Mai magana a madadin AON wato Roland Iyayi, ya ce Ethiopian Airlines zai iya ƙirƙiri farashi mai rahusa, ta yadda zai karya lagon jiragen cikin gida, kuma ya ƙwace masu kasuwa.
Ya yi zargin cewa tuni dama Ethiopian Airlines ke ta ƙoƙarin ganin ya samu ƙofar yin kame-kame a harkokin sufurin Najeriya, domin cika burin sa na ƙwace kasuwar sufurin sama a Afrika baki daya.
“Ethiopia ba za ta taimake ka a kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama a nan Najeriya, yayin da ita kan ta ke da na ta cibiyar a Addis Ababa, babban birnin ƙasar.
A yanzu haka su na gina sabon filin jirgin sama. Zai yi wahala a ga yadda Ethiopia za ta maida hankali wajen kula da Nigeria Air, wanda zai amfani ‘yan Najeriya,” inji Iyayi.
“Mu na tabbatar da cewa mu AON mun san da an kafa Nigeria Air, Farkon abin da Ethiopia za ta fara yi shi ne karya farashi domin ta yi kaka-gida.
“Idan ka karya farashi kuwa to za ka yi galaba kan sauran kamfanonin zirga-zirga na cikin gida. Saboda Ethiopia na da kuɗi danƙare a ƙasa, wanda za su riƙa bindiga da shi su karya farashi har tsawon watanni shida, ta yadda za su gurgunta kamfanonin sufurin jiragen cikin gida.
“Idan su ka yi haka kuwa, to kashi 90% cikin kashi 100% na jiragen ‘yan Najeriya duk durƙushewa za su yi.
“Sannan kuma bayan sun yi kaka-gida sun kore mu daga kasuwar, me zai faru? Za su ƙara farashi ne? To wa gari ya waya kuma?”
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar AON Allen Onyema ya ce irin yadda Ethiopian Airlines ke zumuɗin fara zirga-zirga a ƙarƙashin Nigeria Air, babbar barazana ce a gare su.
“Me zai hana gwamnati ta bai wa kamfanonin sufurin jiragen sama na cikin gida irin goyon bayan da ta bai wa Ethiopian Airlines. Idan aka yi mana haka, ai za mu inganta harkar sosai.” Inji Onyema.
Wasu mambobin ƙungiyar da dama irin su wani mai suna Kashim Shettima na Skyjet sun yi magqnganu.
Shi kuma Daraktan Hukumar Kula da Zirga-zirgar Sararin Saman Najeriya (NCAA), Musa Nuhu, ya ce hukumar sa ta fito da kandagarkin hana Ethiopian Airlines ya kwashe ma’aikatan kamfanonin jiragen cikin gida.
Shi kuwa Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika, ya shaida wa kwamitin cewa Najeriya ba ta da kuɗin da za ta kafa kamfanin na Nigeria Air, shi ya sa ta yi haɗin guiwar mallakar kamfanin tare da Ethiopian Airlines.
Ya ce kuma Najeriya ba ta karya ƙa’idar komai ba. Ta yi haɗin guiwar ce bisa turbar yarjejeniyar ‘Yamoussoukoro Declaration’, kuma yin hakan zai zame wa ƙasar nan alheri.
Ya ce an kafa Nigeria Air ta yadda ba zai bi sahun durƙushewar da irin su Kabo, Okada ko Chanchangi Airline su ka yi ba.
Ya ce ‘yan Najeriya ne za su riƙa tuƙa jiragen da hada-hadar ayyuka a kamfanin, ba Ethiopian Airlines ba.
Sai dai kuma Shugaban Kwamitin Majalisa Nnolim Nnaji ɗan PDP daga Enugu da wasu mambobin kwamitin duk ba su gamsu da wannan haɗin gwiwar kafa Nigeria Air tare da Ethiopian Airlines ba.
Nnaji ya ce rashin daraja ne da faɗuwar girman Najeriya ƙasa warwas a ce a riƙa filfila tutar ta a kan jiragen saman da wata ƙasa ce jagorar sufurin su.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya sha alwashin cewa Jirgin Nigeria Air zai fara tashi cikin Disamba.
Yayin da talakawa a faɗin ƙasar nan ke fama da ƙuncin rayuwa da tsadar abinci da kuma rashin tsaro, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ƙoƙarin kafa kamfanin Nigeria Air an kusa kammalashi da kashi 91 bisa 100.
Buhari ya ce ana kayutata zaton ƙaddamar da shi a cikin watan Disamba, kafin ƙarshen wannan shekarar.
Buhari ya sha wannan alwashin a Taron Bin Diddigin Ayyukan Ministoci na 3 da aka shirya a ranar Litinin, a Abuja.
Ya bayyana cewa kamfanin Zirga-zirgar Jiragen zai fara amfani da tashoshin Legas da Abuja ne, wanda Hukumar Kula da Sararin Saman Najeriya ta amince da su.
Ya ce nan ba da daɗewa ba kuma za a tantance filayen jiragen sama na Kano da Fatakwal domin a ba su satifiket na amincewa da su.
Nigeria Air dai ya lashe naira bilyan 14.6.