Akalla mutum sama da miliyan 500 za su iya afkawa cikin tsanancin rashi lafiya a dalilin rashin motsa jiki a duniya – WHO

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi kira da kakkausar murya da yin gargadi ga mutane cewa lallai a rika fita ana motsa jiki domin akwai yiwuwar miliyoyin mutane za su afka cikin tsananin rashin lafiya a dalilin rashin yin hakan.

WHO ta ce daga shekarar 2020 zuwa 2030 mutum sama da miliyan 500 za su kamu da cututtukan da suka hada da cututtukan dake kama zuciya, ciwon siga, ciwon mantuwa, kiba da dai sauran su a dalilin kawai don basu motsa jikin su yadda ya kamata.

Kungiyar ta ce bisa ga ka’ida kamata ya yi mutum ya motsa jikinsa na akalla mintina 150 duk rana amma yin hakan ma na zama abin wahala ga mutum kashi 27.5% a duniya.

Rashin motsa jiki ya fi yawa a kasashen da suka ci gaba fiye da Kasashen dake tasowa.

A kasashen da suka ci gaba mutum kashi 36.8% ba su motsa jiki sannan a kasashen dake tasowa mutum kashi 16.2% basu motsa jiki yadda ya kamata.

WHO ta ce motsa jiki ba sai mutum ya shiga harkokin wasanni ko tsere-tsere. Za ka iya rika takawa a lokutta masu tsawo, tuka Keke da sauransu duk suna zama hanyoyin motsa jiki da zasu sa a samu lafiya.

Shugabar sashen motsa jiki na WHO Fiona Bull ta ce duniya za ta kashe akalla har Dala biliyan 27 wajen kula da mutanen da suka kamu da cututtuka a dalilin rashin motsa jiki nan gaba.

Fiona ta ce gwamnati za iya amfani da yawan wadannan kudade wajen horar da likitoci miliyan 100 a duniya mai makon sakaci da mutane za su yi saboda kin motsa jiki akai akai su fada cikin matsanancin hali.