Sojoji sun kashe ‘yan bindiga sama da 50 a Kaduna

Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce a dalilin hadin gwiwar rundunar sojin sama da na kasa an samu nasarar kashe ‘yan bindiga sama da 50 a karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.

Aruwan ya fadi haka ne a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Talata a garin Kaduna.

Idan ba a manta ba a ranar Litini Aruwan ya bayyana cewa dakarun Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 10 a kauyen Kwanan Bataru dake bayan garin Fatika a karamar hukumar Giwa.

Ya ce kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari na cikin kananan hukumomin da suka fi fama da hare-haren mahara a jihar Kaduna.

“Dakarun sojojin sun kashe wadannan ‘yan bindiga ne a Saulawa-Farin dake karamar hukumar Birnin Gwari.

“Jirgin saman yaki ya hangi wasu ‘yan bindiga guda biyar akan babura suna shirin kai wa sojoji hari a yanki Saulawa ta gabas. Har wa yau jirgin saman a shawagin da yake yi ya hangi wasu ‘yan bindiga akalla su 50 bisa babura sun doshi yankin Farin Ruwa. Dakarun saman ba su yi wata-wata ba suka darkake su gaba dayan su.

” A kasa kuma Sojoji suka karisa su kaf din su.

” haka kuma yan bindigan da ke yankin Dogon Dawa, Damari da Saulawa sun iske ajalin su inda daga sama sojoji suka yi ragaraga da su.

Gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i ya yaba wa sojojin da ayuukan da suka yi na gamawa da ‘yan bindigan sannan ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da baiwa sojojin hadin goyon baya domin samun nasara a wannan yaki da suka tunkara.