An kama wasu masu kai wa ƴan bindiga man-fetur daga Kano zuwa Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da samar da man fetur ga ƴan bindiga a jihar Katsina, daga Kano, jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Talata, a Kano.

Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin Musbahu Rabi’u, ɗan shekara 31, da Jamilu Abdullahi, mai 37, dukkansu mazauna ƙaramar hukumar Jibiya, jihar Katsina.

  • An kama wasu masu kai wa ƴan bindiga man-fetur daga Kano zuwa Katsina
  • Najeriya za ta yi babban baƙo daga ƙasar Turkiyya

Haruna-Kiyawa ya ce an cafke waɗanda ake zargi ne da motoci ƙirar J5 guda biyu da aka loda musu man fetur cikin jarakuna masu cin lita 25 kuma suka boye su cikin buhunan hatsi da babu komai a ciki.

“A ranar 15 ga Oktoba, 2021, da misalin ƙarfe 12:30 na safe, tawagar‘ ƴan sanda karkashin jagorancin CSP Abubakar Hamma, yayin da suke aikin sintiri a Fagge, Kano, sun tare motocin J5 guda biyu ɗauke da kayan abinci.

“A yayin bincike, an gano jarakuna biyar masu cin lita 25 kowanne cike da man-fetur ɓoye a cikin buhun sukari da babu komai a ciki, cikin ɗayan motocin,” in ji shi.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa “sun zo Kano sau ɗaya daga Katsina, sun sayi man-fetur a cikin jarakunan kuma sun tafi da shi zuwa Jibiya, jihar Katsina inda ya sayar akan farashi mai tsada”.

Wanda ake zargin ya ƙara da cewa, “an kama su ne yayin da suke ƙoƙarin jigilar mai ɗin a karo na biyu.”

DSP Haruna-Kiyawa ya yi bayanin cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Samaila Shuaibu-Dikko, a halin yanzu, ya ba da umarnin yin bincike cikin hankali kan lamarin, bayan haka za a gurfanar da wadanda ake zargi zuwa kotu.

Kwamishinan ya bukaci mazauna jihar da su kula da yanayin da suke ciki sannan su kai rahoton duk wani motsi na mutane zuwa ofishin ƴan sanda mafi kusa.

Ya kuma yi kira ga masu gudanar da gidajen mai a jihar da su guji sayar da mai ga waɗanda ba a san su ba cikin Jarakuna.