Sojoji sun ceto wasu ɗalibai da malaman makarantar Yauri, ɗaliba ɗaya ta rasu

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta ceto daliban makarantar sakandaren mata na gwamnatin tarayya dake Yauri wanda ƴan bindiga suka sace ranar Alhamis.

‘Yan bindiga sun darkaki makarantar suka kwashi ɗaliban da wasu malaman makarantan.

Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar ya shaida a wata sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES cewa ƴan sanda masu gadin makarantar sun yi artabu da maharan har aka harbe jami’i ɗaya.

Ya ce a kan babura su ka darkaki Yauri, amma daga cikin dajin Rijau na Jihar Neja su ka fito, kuma a can su ka nausa da ɗaliban da su ka kwashe.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Onyema Onwachukwu ya bayyana cewa dakarun Najeriya sun yi artabu da maharan a cikin dare da misalin karfe 2:30.

” Ƴan bindigan sun raba kawunansu biyu ne, wasu suka yi Gabas da ɗaliban wasu kuma Yamma da shanun da suka sace.

Bayan wuta da ka yi sa su ta sama da kasa, Allah ya sa annyi nasarar ceto malamai biyu da ɗalibai biyar.

” Haka kuma an kwato shanu sama da 800 daga hannun maharan.

Onyeama ya ce an rasa ɗaliba ɗaya a wannan arangama.

Babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Yahaya ya ce lallai dakaru su matsa har sai sun veto ɗaliban da sauran malaman dake hannun ƴan bindiga.

Satar Ɗalibai: Yadda Karatun Boko Ke Neman Gagarar ‘Ya’yan Talakawa:

Kamar yadda Boko Haram su ka riƙa sace ɗaruruwan ɗalibai a baya, su ka ‘yan bindiga sun bi sawun su wajen yawan kwasar ɗalibai ana yin garkuwa da su.

A cikin 2021 an kai farmaki a makarantun sakandare da su ka haɗa da Jihar Katsina da aka kwashi ɗaruruwan ɗalibai a Ƙanƙara, sai Jihar Zamfara da Jihar Neja inda aka kwashi ɗalibai a garuruwa uku. A Katsina ma an saci ɗaliban Islamiyya 400 kan hanyar komawar su gida tsakar dare daga taron Maulidi.

A lokacin da aka kwashi ɗalibai na baya bayan nan a Kebbi, wasu ‘yan bindiga na riƙe da ɗaliban Islamiyya 139 na Tegina a Jihar Neja.

Sannan jihar Kaduna ta sha fama ita ma da kwashe ɗalibai tun daga na jami’a har zuwa na babbar kwaleji.

Sannan idan ba a manta ba dai a cikin wannan shekarar ‘yan bindiga sun kai samame a Kwalejin Turkish Collage da ke Kaduna, amma sojoji su ka fatattake su.

Yanzu haka akwai wasu ɗaliban Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke hannun ‘yan bindiga. Kuma makarantar da ke Zariya ta kasance a rufe.

Yayin da ba a san adadin yawan ɗaliban Yauri da aka kwashe ba, haka nan kuma ba a san ranar da za a sako su ba. Duk kuwa ya yawan alwashin da jami’an tsaro ke sha cewa su na farautar maharan.