BOKO HARAM: Ba mu da sauran hutu har sai na ga zaman lafiya ya wanzu, ‘yan gudun hijira sun koma gida – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙara jaddada cewa babu sauran hutu a gare su, har sai ya ga cewa an wanzar da zaman lafiya kuma dukkan masu zama a sansanonin gudun hijira kowa ya koma gidan sa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan alwashin a ziyarar da ya kai Maiduguri, babban birnin Jihar Barno a ranar Alhamis.

Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Yayin ziyarar da Buhari ya kai, ya duba yanayin yadda hukumar sojoji ke gudanar da aikin tsaro, sannan kuma ya jinjina wa Gwamna Babagana Zulum, dangane da irin ci gaban da ya samar wa jihar Borno.

Daga nan kuma ya buɗe ayyuka bakwai daga cikin sama da 500 ɗin da Gwamnatin jihar ta ce ta kammala.

“Babu sauran hutu a gare mu har sai bayan mun samar da tsaro, sannan kuma dukkan masu gudun hijira duk sun koma gidajen su.

“Ba zan taɓa mantawa ba a rayuwa ta cewa Jihar Barno ce aka fi ba ni ƙuri’u mafi yawa har kashi 90 bisa 100 na ƙuri’un da aka jefa na zaɓen shugaban ƙasa a jihar.

“Abin da aƙalla zan ci gaba da yi maku shi ne na tabbatar na maido maku da zaman lafiya a Arewa maso Gabas da sauran yankunan ƙasar nan baki ɗaya.”

“Ina cike da matuƙar farin cikin kasancewa tare da ku a wannan ziyara da na kawo, saboda ni tuni na maida Maiduguri da jihar Barno tamkar gida. Domin a nan na yi gwamna a Jihar Barno shekaru 46 baya.

“Sai dai kuma rashin jin daɗin da na ke yi, na so a ce wannan ziyara na kawo ta ne a yanzu a lokacin zan so ana cikin zaman lafiya ne na zo.”

Buhari ya nuna cewa irin hare-haren da ‘yan ta’adda su ka riƙa kaiwa kwanan baya, sun nuna har yanzu akwai sauran rina a kaba.

“To dalili kenan na kawo wannan ziyara domin na ƙarfafa ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya nan ba da daɗewa ba wanann yanki.

Buhari ya ce dukkan manyan Hafsoshi Sojojin da ya naɗa kwanan nan gogaggu ne, kuma duk sun jagoranci wani ɓangare ko ɓangarori na yaƙi da ta’addanci a baya.