SAURIN FUSHI: ‘Kani’ ya kashe ‘Wa’ saboda naira 1,500 kuɗin wutar lantarki

Wani magidanci mai suna Peter Orji cikin fushi ya bindige Wan sa da dalilin kin rashin biyan kuɗin wuta naira 1,500.
Peter Orji ƙanin Godwin Orji ne kuma suna na zaune ne a gida ɗaya amma kowa da nashi bangaren.
Majiya ta shaida cewa Peter ya fusata ne bayan Wansa Godwin ya yanke masa wutar lantarki saboda kin biyan nashi kuɗin wutan da ake biya duk wata.
Cikin fushi sai Peter ya koma cikin gidan sa ya ɗauko bindiga ya bindige Godwin.
Kakakin ƴan sanda jihar Anambra Tochukeu Ikenga ya tabbatar da aukuwar abin sannan ya kara da cewa za su tuni Kwamishinan jihar ya umarci a mika Peter ga sashen binciken manyan laifuka da rundunar.
Bayan haka an gano ashe ba tun yanzu ba ƴan uwan biyu suna zaman doya da manja ne a tsakanin su. Basu jituwa.
Rundunar ta ce ta kama matar Peter tun farko sannan daga baya ta kama shi kan sa Peter.