ZAZZABIN LASSA: Mutum 894 sun kamu, cutar ta yi ajalin mutum 168 a Najeriya

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa a shekarar 2022 mutum 894 sun kamu da zazzabin Lassa sannan mutum 168 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar a Najeriya.

Bisa ga rahoton yaduwar cutar da hukumar ta fitar na mako 33 ya nuna cewa an yi wa mutum 6,392 gwajin cutar a kananan hukumomi 101 dake jihohi 25 a kasar nan.

Jihohin Bauchi, Ondo da Edo na da kason kashi 70% daga cikin yawan mutanen da suka kamu da cutar.

Jihar Ondo 31%, Edo- 26% da Bauchi-13%.

Adadin yawan mutanen dake kamuwa da cutar a mako ya ragu daga mutum 9 zuwa mutum 5 a mako 32 a jihohin Ondo da Edo.

Cutar ya fi kama mutane masu shekara 21 zuwa 30 sannan mata sun fi maza yawa wajen kamuwa da cutar.

A mako 33 babu jami’in lafiyan da ya kamuwa da cutar a Najeriya.

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Ƙasa NCDC ta bayyana cewa a cikin mako na 32 da daga ranar 8 zuwa 14 ga Agusta 2022 mutum 9 sun kamu da zazzabin Lassa kuma cutar ta yi ajalin mutum 3 a kasar nan.

NCDC ta ce an gano haka ne bayan gwajin cutar da aka yi wa mutum 178 da ake zargin sun kamu da cutar.

Sakamakon gwajin ya nuna cewa mutum 9 sun kamu da cutar inda a ciki akwai jami’in kiwon lafiya daya.

An gano wadannan mutane a jihohi uku da suka hada da Ondo, Edo da Enugu.

Hukumar ta ce yaduwar cutar ya fara raguwa daga makon 31 inda a makon mutum 13 suka kamu zuwa mutum 9 a mako 32.

Mecece zazzabin Lassa

Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai a sannu a hankali tana ta afkawa mutanen kasar nan.

Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.

Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar kuma ba a gaggauta neman magani ba.

ALAMUN KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA

Ciwon kai: Yawaita fama da ciwon kai alama ne cewa lallai sai an duba mutum a asibiti, domin idan zazzabin lassa ta kama mutum ciwon kai na daga cikin alamun dake fara nunawa.

Zazzabi: Za a rika jin jiki yayi nauyi kamar zazzabi-zazzabi haka idan Lassa ta shiga jikin mutum. Zazzzabi ko masassara zai rika damun mutum a wannan lokaci.

Ciwon jiki: Jikin mutum zai rika yawan yi masa ciwo matuka. Ko ina zai rika jin ciwo yake masa. Hakan ma alama ce dake nuna an kamu da Lassa. Hakna kuma sun hada da ciwon gabobin, ciwon baya, yawan gajiya sannan a wasu lokutan har da ciwon kafafu.

Amai: Saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum kuma zai rika yawan yin amai.

Rashin iya cin abinci: Zazzabin lassa na hana mutum iya cin abinci. zaka ci gaba daya baka bukatan cin wani abu duk ko da cewa zaka rika jin yunwa.

Yawan yin Bahaya: Za a yi fama da yawan shiga bandaki a dalilin kamuwa da wannan cuta sannan hakan zai sa mutum yawan jin kishin ruwa.

Yawaita Suma: Idan har mutum ya kamu da wannan cuta, za a rika yawan suma saboda rashin lafiyar dake jikin mutum.

Jini: Za a rika zubar da jini ta wasu kafafen jiki musamman idan abin ya fara nisa ba a duba mutum a asibiti. Hakan na nuni cewa cutar ta fara yi wa mutum mummunar illa.

Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da Zazzabin Lassa

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

5. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

6. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

7. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

8. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

9. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

10. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

11. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.