Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi ya gana da shugaban mulkin soja na Nijar, Janar Tchiani

Shugaban mulkin soja na Nijar ya gana da sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi a Nijar.
Ganawar Janar Abdourahmane Tchiani da Sarki Sanusi ya zo ne a daidai shugaban ya ki ganawa da duka tawagar ECOWAS na Amurka da na Najeriya.
Bayan tattaunawar, Sanusi tare da janar Tchiani da tawagar sa sun dauki hotuna.
Majalisar Ƙolin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta bayyana cewa ba ta goyon bayan ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar takunkumin karya mata tattalin arziki, kuma ba ta yarda a afka wa Nijar da yaƙin ƙwatar dimokraɗiyya daga hannun sojojin mulki ba.
“Sanannen abu ne cewa irin wannan takunkumi ba ya haifar da wani alheri, sai ma ƙuntata wa waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.”
Haka NSCIA ta bayyana a cikin wata kakkausar sanarwa da ta fitar, wadda Mataimakin Babban Sakataren majalisar, Salisu Shehu ya sanya wa hannu.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ne shugaban majalisar, wadda ta ce ba ta goyon bayan a yi amfani da ƙarfin soja domin a kawar da sojojin juyin mulkin da suka hamɓaras da Gwamnatin Mohammed Bazoum, a cikin watan Yuli.
ECOWAS a ƙarƙashin shugaban ta, kuma Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumin da ya haɗa da rufe kan iyakokin Nijar da kuma kulle asusun duk wani ɗan uwa ko mai goyon bayan shugabannin mulkin sojan Nijar a dukkan Manyan Bankunan Kasashen ECOWAS.
NSCIA ta nuna damuwa ganin yadda Sojojin juyin mulkin Nijar su ka yi kunnen-uwar-shegu da kiraye-kirayen da ake yi masu.
To sai dai kuma ta ce duk da haka, ba ta goyon bayan a afka wa ƙasar da yaƙi, a yi sulhun diflomasiyya shi ne mafi alheri.
Sultan na Sokoto wanda shi ne Shugaban NSCIA, ya na cikin tawagar da ECOWAS ta aika Nijar cikin makon da ya gabata, a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, amma mahukuntan sojan ƙasar ba su yi masu kyakkyawar tarba ba.