Kamfanin Azman ya dakatar da aiki, ya dakatar da ma’aikatan sa su tafi hutun dole

Kamfanin jiragen sama na Azman ya dakatar da aiki sannan ya tura ma’aikatan sa duka su fara hutun dole ba tare da albashi ba.
Kakakin Kamfanin Nurudden Aliyu ya ce Kamfanin da yanke wannan shawara ne domin ta gyara jiragen saman da ake aiki da su sannan da yadda farashin kaya ya kara kudi.
“Muna sa ran cewa jiragen saman dake wurin gyara za su dawo su fara aiki a cikin farkon makon watan Oktoba.
Manajan ma’aikatan kamfanin Magaji Misau ya ce ma’aikatan Kamfanin za su tafi hutu daga ranar daya ga Agusta 2023.
Ya ce manyan ma’aikata 8 daga cikin ma’aikatan Kamfanin ne za su ci gaba da aiki a Kamfanin.
A watan Satumban bara dai Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA) ta dakatar da kamfanin daga aiki a Najeriya saboda kin sabunta lasisinsa na AOC.
Lasisin dai ya kare ne tun a watanni uku na farkon shekara ta 2022.