BINCIKEN HARƘALLAR ƊAUKAR MA’AIKATA: Hukumomi da Cibiyoyi da Ma’aikatu 35 sun ƙi bayyana a gaban kwamitin bincike

Aƙalla hukumomin gwamnati da cibiyoyi na ma’aikatun Gwamnatin Tarayya har 35 ne su ka noƙe, tare da ƙin bayyana a gaban Kwamitin Binciken Harƙallar Ɗaukar Ma’aikata a Cibiyoyi, Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Tarayya a Majalisar Tarayya.
Kwamitin wanda Honarabul Yusuf Gagdi ke shugabanta, ya nuna ɓacin rai ganin yadda a ranar Laraba an gayyaci cibiyoyi ma’aikatu da hukumomi 40 su halarta, amma ɗaya tal kaɗai ya bayyana a gaban kwamitin.
An kafa kwamitin ne domin tantance ma’aikatan da aka ɗauka ta hanyar cuwa-cuwa, ba bisa ƙa’ida ba, ganin yadda zargi da ƙorafe-ƙorafen sayen takardar shaidar ɗauka aikin gwamnatin tarayya ke ta fitowa a fili.
Wannan cuwa-cuwa dai ta na kawo cikas da aringizon maƙudan kuɗaɗe a tsarin biyan albashin bai-ɗaya na IPPIS.
“Yawancin ma’aikatu da hukumomin nan ba su ganin darajar gwamnati. Shi ya sa su ka ƙi zuwa gayyatar da muka yi masu. Kamata ya yi a ce yau an samu ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomi 40. Amma gudu huɗu kaɗai su ka bayyana.” Cewar Gagdi a cikin fushi.
A baya ma an nemi wasu hukumomi su turo wasu Daraktoci ko Jami’ai, amma ba su tura ba.
Tone-tonen Asiri Tsakanin Shugabar Hukumar FCC Da Hadimin Ta A Gaban Kwamiti:
‘Ni ke dillancin sayar da takardun shaidar ɗauka aiki, ina kai kuɗin ga Shugabar Hukuma’ – Hadimin Shugabar FCC:
Za iya cewa zaman Kwamitin Majalisar Tarayya mai binciken harƙallar ɗaukar ma’aikata a Hukumar Daidaiton Ɗaukar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, ya zama zaman tonon silili.
A zaman da kwamitin ya yi a ranar Talata, tsohon Hadimin Shugabar Hukumar Daidaiton Ɗaukar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, mai suna Haruna Kolo, ya fallasa yadda Shugabar Hukumar, Muheeba Ɗankaka, cewa ita ce ta riƙa ba shi takardun shaidar ɗaukar aikin Gwamnatin Tarayya, ya na sayarwa, kuma ya na kai mata kuɗin har gida.
A ranar Litinin Kolo ya yi wannan bayani a gaban kwamitin majalisar tarayya, mai binciken harƙallar ɗauka aiki a hukumomin gwamnatin tarayya.
A shaidar da Kolo ya bayar, ya ce Muheeba Ɗankaka ce ta naɗa shi gogarman masu yi mata dillancin sayar da takardun ɗauka masu neman aiki, su na karɓar maƙudan kuɗaɗe daga hannun su.
Ya ce ana tura kuɗaɗen ta cikin asusun ajiyar sa na banki, amma ita sai dai ya je POS ya cira ya kai mata har gida.
“Ita Shugabar Hukumar ce da kan ta, ta wakilta ni da haɗa kai da wani Shehu, wanda direba ne kuma PA na wani kwamishinan jihar Taraba.
“Aiki na shi ne ina duk wanda za a ɗauka aiki, Ni ke kai wanda aka ɗauka IPPIS domin a yi masa rajista a manhajar sunayen masu karɓar albashi. Kuma dama ita ce kaɗai ke sa hannu a takardar shaidar ɗaukar ma’aikaci. Idan ta sa hannu, ni ke kaiwa Ofishin Akanta Janar, domin a shigar da shi jerin masu karɓar albashi (IPPS).
“Duk wanda za a ɗauka aiki, sai ya biya kuɗi ta asusun ajiyar banki na tukunna. Ba sanin daga inda su ke na ke yi ba, amma Shehu ne ke kawo su a wuri na. Wasu su kan biya Naira miliyan 1, wasu har Naira miliyan 1 da 500,000, a asusun ajiya ta da ke Eco Bank.
“To amma ita idan ta tashi karɓar kuɗaɗen, sai na je POS na ciro ruwan kuɗi na kai mata har gida.” Inji Kolo.
Ya ce Muheeba Ɗankaka ta yi masa sakayya da samar masa aiki a Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnatin Tarayya (AMCON), shi da wasu mutum uku.
Ya ce a cikin waɗanda aka ɗauka aikin har da wani ƙarin ita shugabar hukumar.
“Cikin waɗanda ta samar wa aiki a AMCON ɗin kuwa, a cikin mu akwai wata mai suna Khadijah Olushola. Amma ita Khadijah ba a ɗauke ta ba. Sai Shugabar Hukuma ta zarge ni wai ni ne na shirya makircin da ya yi sanadiyyar ƙin ɗaukar ƙanwar ta aikin.”