Sannun Ku Da Kokari: Shugaban Majalisar Dattawa ya ce Manyan Hafsoshin Tsaro na aiki tukuru

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan ya jinjina wa Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya da sauran shugabannin bangarorin tsaro bisa aiki tukurun da ya ce su na yi domin dakile matsalar tsaro a fadin kasar nan.

Wannan jinjina da yabo sun zo ne jim kadan kafin majalisa ta fara ganawa da shugabannin tsaro a sirrance a ranar Alhamis a zauren majalisar.

Lawan ya ce jami’an tsaron Najeriya na matukar kokari, kuma ana gamsuwa da aikin su a cikin wannan yanayi da su ke amfani da iyar kayan aikin da ke hannun su.

“Ku na aiki tukuru wanda kowa ya shaida domin har ana samun masu rasa rayukan su sosai a cikin jami’an tsaro a wannan sadaukarwa da ku ke yi.

“Saboda haka a koda yaushe Majalisar Dattawa na tare da ku domin a gudu tare a tsira yare.” Inji Lawan kafin su fara ganawar sirri da manyan shugabannin tsaron.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Majalisar Dattawa na ganawar sirri da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya.

A yanzu haka Manyan Hafsoshin Tsaro na Kasar nan na can na ganawa da Manyan Hafsoshin Tsaron kasar nan da kuma sauran shugabannin fannonin tsaro.

Sun amsa kiran gayyatar da Majalisar Dattawa ta yi masu ne, domin su yi bayanin halin da ake ciki kan tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Wadanda su ka halarta sun hada da Babban Hafsan Tsaron Kasa, Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojojin Kasa Ibrahim Attahiru, na Sama Awwal Gambo da na Ruwa.

Haka kuma cikin sauran manyan shugabannin tsaron akwai Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Baba Usman.

Sun shiga dakin taro kuma an kulle kofa wajen karfe 11:06 na rana. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ne zai wa manema labarai jawabi bayan sun kammala taron.

Sannan kuma Majalisar Dattawa ta amince shugabannin majalisar su ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari domin su tattauna gaskiyar lamarin halin da kasar nan ke ciki, ta yadda za a shawo kan munin da tabarbarewar tsaron ta yi.

Tun a ranar da aka gayyaci shugabannin tsaron, sai da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi roko ga sauran santoci cewa idan sun amsa gayyata sun zo yau ranar Alhamis, to idan sun yi kukan rashin isassun kudaden aikin tsaro, to a amince a kasa dumbuza masu.

Najeriya na ci gaba da afkawa cikin mawuyacin halin tabarbarewar tsaro, ta yadda a kullum ana kashe mutane da dama, kuma ana sace wasu masu yawa ana yin garkuwa da su.

Sai dai kuma a ranar Laraba Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya maida wa jam’iyyar PDP raddin cewa aikin gurfanar da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga, na jihohin da abin ya yi wa katutu ne, ba aikin gwamnatin tarayya ba ne.

Ya ce gurfanar da ‘yan ta’adda ne aikin gwamnatin tarayya.