Buhari ya dakatar da shugabar hukumar tashohin jiragen ruwa

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa (NPA).

Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito an maye gurbin shugabar da Daraktan kuɗi na hukumar Muhammad Bello Koko.

Izuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance dangane da dakatarwar.