RAHOTON MUSAMMAN: ‘Yan bindiga sun ƙi karɓar kuɗin fansa domin su saki mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara

‘Yan bindigar da su ka sace mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara sun raina kuɗin fansar da aka ba su, saboda haka sun ƙi sakin sa.

An dai kama mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara Honorabul Nasiru Magarya tun a farkon watan Agusta, a wani farmaki da ‘yan bindiga su ka kai a Magarya.

An kama shi tare da wasu mutum biyar da su ka haɗa har da matar mahaifin na sa, a Magarya da ke cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Wasu jami’an gwamnati sun nemi gogarman ‘yan bindiga Halilu Kachalla domin ya shiga tsakani, ya taimaka waɗanda su ka kama mahaifin kakakin su sake shi.

Wani hadimin Kakakin Majalisar Zamfara ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an gayyaci Kachalla ya ne ta hannun wani jami’in Ƙaramar Hukumar Shinkafi.

‘Yan Bindiga Sun Raina Kuɗin Fansa

Wani hadimin Kakakin Majalisar Zamfara ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa makusancin kakakin ya samo kuɗi kamar yadda ‘yan bindiga su ka nema.

“Tsohon Kwamishina wanda ɗan Zurmi ne ya na a sahun gaba wajen sasantawar. Shi ma Halilu Kachalla ya yi bakin ƙoƙarin sa, amma ka san ya na da matsala da sauran ‘yan bindiga, saboda a yanzu ya fi kusa da gwamnatin Zamfara.

“Sai shi tsohon kwamishina ya shaida wa Kakakin Majalisa cewa za su biya kuɗin kawai, tunda Kachalla ya kasa taimakawa a sako mahaifin kakakin.”

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa bai san ki nawa maƙudan kuɗaɗen da aka haɗa wa ‘yan bindigar ba.

“Abinda kawai na sani, wasu mutane daga Zurmi da Shinkafi sun ɗauki kuɗi sun kai a sansanin gogarma Turji, amma ba ma ko samu ganin sa ba. Sun dai gana da wani kwamandan sa mai suna Ɗan Bukkolo, wanda shi kuma ya shaida masu cewa umarnin da Turji ya ba shi kawai idan sun zo su koma da kuɗin.”

Lamarin ya faru kwana kaɗan bayan ‘yan bindiga sun sake yin tattaki har Magarya, su ka ƙone gidaje da dama, ciki har da gidan mahaifin Kakakin Majalisa wanda ke a hannun su da kuma wani gidan kawun kakakin.

Wakilin mu ya kasa samun Kakakin Yaɗa Labarai na Kakakin Majalisar Zamfara, mai suna Mustafa Ƙaura, domin jin halin da ake ciki, saboda matsalar kulle lambobin wayoyi da aka yi a Zamfara.