SANATA NDUME YA BUƊE WA TALAKAWA WUTA: Ya ce watandar Naira miliyan bi-biyu ba wata tsiyar da za a riƙa yi masu kwakwazo ba ce

Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya yi wa masu ƙorafin watandar Naira miliyan bi-biyu da aka yi wa Sanatoci, a matsayin kuɗin jin daɗin dogon hutun da za su yi.
Sanatocin dai sun tafi hutu, sai ranar 26 Ga Satumba za su koma aiki.
Da ya ke magana da Sashen Hausa na BBC, Ndume ya ce bai ga dalilin da zai sa a riƙa kwakwazo, caccaka da yamaɗiɗi ba don an ba kowane Sanata Naira miliyan biyu kuɗin hutu.
“Kuɗin nan fa haƙƙin mu ne, ba wata rufa-rufa aka yi ba. Ana yi wa abin wani kallo ne saboda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi ɓarin-baki ya sanar da bayar da kuɗaɗen a fili, a zauren Majalisa.
“Waɗannan kuɗaɗe fa kamar kuɗin hutun da ake bai wa ma’aikata ne idan ma’aikaci zai tafi hutu. To mu na kuɗaɗen tafiya hutun ne aka ba mu. Kuma haƙƙin mu ne.
Ya ƙara da cewa shi bai ga wani dalilin da zai sa don an raba Naira miliyan 218 ga Sanatoci 109 har a riƙa surutai ba.
Ndume ya ce duk Godswill Akpabio ne ya janyo masu wannan yamaɗiɗi, lokacin da ya yi kasassaɓar bayyana kuɗaɗen a fili.
“Saboda Akpabio ya nuna kamar wasu buhunan maƙudan kuɗaɗe ne aka liƙa jigila ana yi mana watanda.
Ndume ya ina tsiya ina Naira miliyan biyu ga Sanata ɗaya, a matsayin kuɗin hutu?
Ya ce sanatoci na tunanin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki kan Akpabio, wanda ya fallasa kuɗaɗen a bainar jama’a.
“Bayan an tashi sai da na gargaɗe shi, na ce bai kamata ya bayyana watandar kuɗaɗen kowa ya ji ba”, cewar Ndume.