ALƘAWARIN TINUBU GA ‘YAN NAJERIYA: ‘Ba za a sake ƙara farashin fetur ba’

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ba za a sake ƙara wa ‘yan Najeriya farashin fetur ba.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Tinubu ne, Ajuri Ngelale ya bayyana haka a Abuja ga manema labarai, bayan ya yi wata ganawar sirri da Tinubu, a ranar Talata.
“Shugaban Ƙasa na tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba za a ƙara wa fetur kuɗi ba, kamar dai yadda NNPCL ya yi sanarwar haka a jiya Litinin.” Haka Ngelale ya ce.
“Muna ƙara nanatawa, Shugaban Ƙasa ya tabbatar cewa ba za a ƙara wa litar fetur farashi ba.”
Haka kuma Tinubu ya ce akwai wata matsala da ke tattare da harkokin fetur wadda ke ruruta wutar batun ƙarin kuɗin fetur.
Daga nan ya yi alwashin cewa za a toshe duk wasu ƙofofi ko ramukan da matsaloli ke bi su na shiga, har ake samun cikas wajen wadatar da fetur ko’ina a Najeriya.
Farashin fetur dai ya riƙa tuma tsallen gada ya na yin sama, daga Naira 200 kowace lita, har sai da ya dangana da Naira 617 cikin ƙanƙanen lokaci.
Wannan ne ya haifar da ƙarin kayan abinci da sauran kayayyaki, tare kuma da ƙara ruruta raɗaɗin tsadar rayuwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
Har yau kuma tallafin rage raɗaɗin rayuwar da Tinubu ya ce za a raba marasa galihu bai isa gare su ba, a inda ma aka raba a wasu jihohin, tallafin ko jiƙa maƙoshi bai ishe su ba.
Har yau Najeriya na shigo da tataccen fetur ne daga ƙasashen waje, ga shi kuma a cikin ƙasa ana fama da tsadar dala, daidai lokacin da martabar Naira ke ci gaba da zubewa. Dalili kenan ‘yan Najeriya ke hasashe da fargabar cewa farashin fetur zai iya tashi kwanan nan.
To sai dai kuma NNPCL ma ta ƙaryata ji-ta-ji-tar yiwuwar ƙarin kuɗin fetur, kamar yadda ta yi sanarwar da wannan jarida ta buga tun a ranar Talata.
Yayin da ƙungiyoyin ƙwadago su ka yi barazanar tafiya yajin aiki, Ngelale ya ce babu wani dalilin da zai sa su yi wannan barazanar.
Sai dai kuma ya tabbatar da cewa ba gaskiya ba ce da ake yaɗa wata ji-ta-ji-ta cewa gwamnati za ta dawo da biyan tallafin fetur, wanda ta cire.