RIKICIN NIJAR: Ɗan Bazoum na fama da ‘matsananciyar rashin lafiya’

An bayyana wa Shugabannin ECOWAS cewa Salem, ɗan hamɓararren Shugaban Nijar, ya na fama da ‘matsananciyar rashin lafiya’.
An shaida masu hakan ne yayin taron da su ka gudanar a ranar Alhamis, kamar yadda wani jami’i ya gulmata, wanda ke wurin a lokacin da aka tayar da maganar.
An shaida wa Shugabannin ECOWAS cewa Salem ya rame, har nauyin sa ya ragu da kilo 10, tun bayan tsare shi da aka yi, tare da mahaifin sa bayan juyin mulkin ranar 26 Ga Yuli a Nijar.
ECOWAS da sauran ƙungiyoyin ƙasashen waje da dama, sun nemi a gaggauta sakin Bazoum, Salem sauran iyalan Bazoum da dukkan jami’an gwamnatin sa da ke tsare.
A ranar Juma’a shi ma Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken, ya shaida wa tsohon Shugaban Nijar, Mohammed Issoufou “damuwar sa” dangane da ci gaba da tsare Bazoum da iyalan sa a cikin “mummunan yanayi”.
Blinken ya ce ya damu ƙwarai ganin yadda Sojojin juyin mulkin Nijar su ka ƙi sakin Bazoum da iyalan sa, wanda sakin na sa zai nuna wani halin dattako daga ɓangaren sojojin.
Wata ‘yar Bazoum mai suna Zazia Bazoum, ta shaida wa jaridar Guardian ta Ingila cewa iyalan su na rayuwa a cikin wani mawuyacin hali.
Ta ce mahaifin ta Bazoum ya zabge da kilo biyar, mahaifiyar ta ma ƙibar ta ta ragu da kilo biyar, yayin da ɗan uwan ta Salem ya zabge da kilo 10.
Ran ECOWAS ya ɓaci matuƙa ganin yadda mahukuntan sojan Nijar ba su yi wa tawagar Abdulsalam Abubakar kyakkyawar tarba ba.
A taron ranar Alhamis a Abuja, ƙasashen Senegal, Cote d’Ivoire da wasu ƙasashen sun goyi bayan a afka wa Nijar da yaƙi domin a maida gwamnatin farar hula da ƙarfin tuwo.
Shugaba Alassane Ouattara ya shaida wa Shugabannin ECOWAS cewa gwamnatin ƙasar sa za ta iya samar da gudummawar dala miliyan 150 domin tallafa wa dakarun yaƙar Nijar da hidimar zirga-zirgar sojojin.