‘Sama ba zai faɗo ba’ idan Kotu ta kwace kujerar shugaban kasa ta ba Atiku – Kadaɗe

Shugaban Matasa na jam’iyyar PDP, Mohammed Kadade ya bayyana cewa sama ba zai fado ba idan kotu ta soke zaɓen Tinubu, a Shari’ar da ake yi yanzu haka.
Kadade ya ci gaba da cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, shi ne halastaccen wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
A bidiyo da ya saka a shafin sa na sada zumunta a yanar gizo ranar Juma’a, Kadade ya ce hukuncin kotun zai yi tasiri matuka a dorewar dimokuraɗiyyar kasar nan.
” Mu gani yanzu cewa gwamnati da ke mulki bakuwa ce, da sauran ta. Hakan ya nuna tun daga yadda su ka fara da cire tallafin mai ba tare da samar da mafita ga talakawa.
” Najeriya na cikin halin ha’ula’i, tattalin arziki kasa ya tabarbare, saboda an dora wadanda ba su san yadda ake mulki ba. Sabon Shiga aka ba. Kuma mun ga yadda ƴan Najeriya suka fito suka yi zaɓe amma aka dora musu wanda ba shi suka zaɓa ba.
Abinda muke jira shine kotu ta tabbatar wa ƴan Najeriya wanda suka zaɓa, wato Atiku Abubakar na PDP. Idan ta yi haka shi ne daidai, kuma sama ba zai faɗo ba don ta tsige Tinubu.
Atiku na PDP da Obi na LP na kalubalantar nasarar da Bola Tinubu ya yi a zaben shugaban kasa na 2023.Dukkan su sun ce su ne suka yi nasara a zaɓen.