TSAUTSAYI BA YA WUCE RANA: ‘Yan bindiga sun kwashe ‘yan NYSC takwas a Zamfara, kan hanyar su ta zuwa Sokoto daga Akwa Ibom

Wasu ‘yan bindigar da su ka tare hanya, sun kwashe ‘yan bautar ƙasa (NYSC) su takwas a Zamfara, kan hanyar su ta zuwa aikin bauta wa ƙasa a Jihar Sokoto daga Akwa Ibom.
Dukkan waɗanda aka yi garkuwar da su, su na cikin wata motar bad ta Kamfanin Sufurin Motocin Akwa Ibom (AKTC), daga Uyo, kan hanyar zuwa aikin bautar ƙasa a jihar Sokoto.
Majiya daga kamfanin sufurin AKTC ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an sace matafiyan ranar Litinin da jijjifin safiya.
Majiyar wadda ba ta so a bayyana sunan ta, ta ce ‘yan NYSC ɗin dai su 11 ne, amma uku sun tsira, aka kama takwas.
‘Yan bindigar sun kuma kama direban motar wadda ke ɗauke da su.
“An sauke ‘yan bautar ƙasar daga cikin motar da su ke ciki, daga can kuma aka nausa cikin daji da su.”
“Sun bar nan Uyo tun a ranar Juma’a, suka kwana a Abuja. To sun shiga Jihar Zamfara, kafin su isa Sokoto aka yi garkuwa da su.”
Ya ce an sanar da jami’an gwamnati da jami’an tsaro sace ‘yan bautar ƙasar da aka yi.
Daga cikin waɗanda aka yi garkuwar da su akwai Emmanuel Esudue, kuma dukkan su wayoyin su a kashe su ke tun a ranar Alhamis.
Sannan kuma akwai wata mai suna Betty Udofia.
Sai dai kuma wani mai suna Edidiong Richard, ya rubuta a shafin sa na Facebook cewa ‘yan bindigar sun tuntuɓi iyayen Udofia, inda har su ka nemi sai an biya su fansar Naira miliyan 4 tukunna kafin su sake shi.
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce zai tabbatar da faruwar lamarin tukunna, kafin ya waiwayi wakilin mu.
An kuma tuntubi Kakakin Yaɗa NYSC, Eddy Megwa, amma bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba.