Atiku ya yaba wa Farfesa Gwarzo kan samun lasisin kafa sabbin jami’o’i biyu da ya samu daga NUC

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjina wa shugaban rukunin jami’o’in Maryam Abacha dake Kano da Nijar bisa kara samun dama da yayi na kafa sabbin jami’o’i har biyu a kasar nan.
Tun a farkon wannan shekara ne Hukumar Kula da jami’o’i na Kasa, NUC, ta amince da Kafa Jami’ar Kanada ta Najeriya, Abuja da Jami’ar Franco-British a Kaduna.
Farfesa Gwarzo ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democracy Party, Atiku Abubakar a ofishin sa a ranar Alhamis domin nuna masa lasisin sabbin jami’o’i biyu da aka amince da su wanda shine ya kafa su.
Farfesa Gwarzo ya ba da gudunmawa sosai ga ci gaban ilimi a Najeriya da ma Nahiyar Afrika.
Atiku ya ce ” Wannan ziyara na karamci da Farfesa Gwarzo ya yi min abin a yaba ne. Bayan haka ya nuna min takardar shaidar amincewa da kafa sabbin jami’o’i har biyu wanda hukumar NUC ta amince masa. Na ta ya shi murna sannan kuma ina alfahari da shi bisa irin gudunmawar da yake baiwa harkar ilimi a nahiyar Afirka.