Sake fantsamar cutar korona a Turai, Rasha da Chana ta fara karya farashin gangar ɗanyen mai a duniya

Bayan tashin gwauron zabin da farashin gangar ɗanyen man fetur ta yi a duniya a kwanan baya, har ana tunanin kafin ƙarshen shekarar nan za ta iya kai dala 100 duk ganga ɗaya, a ranar Alhamis ɗin nan kuma farashin ya sake yin ƙasa kusan yadda ya ke ƙasa a makonni biyu da su ka gabata.
Haka kuwa ya faru ne saboda sake fantsamar cutar korona a ƙasashen Turai ta Yamma, Rasha da kuma wasu sassan yankunan Chana.
Karyewar farashin ya fara sa masu murnar cewa tattalin arzikin ƙasashe zai yi saurin farfaɗowa, guyawun su sun yi sanyi sosai, domin cutar korona na haddasa raguwar bukatar mai a duniya.
Buƙatar na raguwa sakamakon taƙaita zirga-zirga, bulagulo da tafiye-tafiye waɗanda ba su zama na tilas ba a motoci da jiragen sama.
Haka kuma manyan jiragen ruwa masu jigilar kayan safara daga wannan ƙasa zuwa waccan, su na dakatar da lodin kaya zuwa ƙasashen da korona ta shafa.
A ranar Alhamis ɗin nan farashin gangar ɗanyen mai samfurin ‘Brent’ ya koma dala 83.64.
Shi kuwa samfurin ɗanyen mai na Amurka ya koma dala 82.77, kuma ana ganin farashin zai ƙara yin ƙasa, bisa la’akari da irin yadda ake samun rahotannin sake fantsamar cutar korona.
Ƙwararrun masana biyu kan hada-hadar ɗanyen mai a duniya, waɗanda ke Kamfanin Bincike na ANZ, wato Daniel Hayes da Sonori Kumari, sun ce lamarin zai kashe kaifin kuzarin da ake na ganin tattalin arzikin duniya ya farfaɗo da wuri, tun bayan dukan da ya sha a hannun korona a cikin 2020.
A Najeriya, PREMIUM TIMES Hausa ta buga nazarin yadda rashin iya tace ɗanyen mai a matatun Kaduna, Warri, Fatakwal da ta Legas, ya sa a yanzu ƙasar ta bayyana cewa ta dogara ne ga matatar fetur ɗin da Aliko Ɗangote ke ginawa a Legas, domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya ce idan Ɗangote ya fara tace ɗanyen mai nan a gida, to gwamnatin tarayya za ta riƙa saye da naira a hannun sa, maimakon kwasar daloli ana sayo tataccen fetur daga ƙasashen Turai.