Mun fada cikin tsananin talauci da mawuyacin hali dalilin zaman ‘Kulle’ da IPOB suka kakaba a jihohin mu – Direbobin Abia

Direbobin motocin haya dake Umuahia jihar Abia sun yi kira ga kungiyar IPOB da ta raba musu tallafi domin rage radadin tsananin talauci da suka fada saododa dokar zaman gida dole da IPOB ta saka a fadin jihar.

Direbobin sun ce dokar zaman gida da kungiyar IPOB ta saka ya fi shafar fannin sufuri a jihohi biyar dake yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.

Babbar matsalar ma ita ce idan ka yi kokarin dan fitowa ka nemi abinci ko wani abu da ‘yan kungiyar za su tare ka su zabzabga maka bulala sannan su kora ka gida.

Mazaunan garin Umuahia sun ce kungiyar IPOB ta canja dokar zaman gida daga zama a gida duk ranar Litini zuwa duk ranar da kotu za ta zauna yin Shari’ar shugaban kungiyar Nnamdi Kanu amma duk ranar Litini mutane na tsoron fitowa saboda gudun kada su sha bulala daga IPOB.

Shugaban kungiyar Direbobin motocin haya na jihar Henry Okezie ya ce: “Akwai ranar da muka ce za mu fita aiki duk da dokar da suka saka amma fa bamu ji da dadi ba. Sun lalata mana motoci sannan sun zazzane wasu direbobin.

“Dole mu fita nema saboda da dama daga cikin mu sun karbo hayan motocin su ne.

“A rana mukan yi cinikin Naira 10,000 sannan a duk ranar da ba mu yi aiki ba mukan yi asarar sama da naira miliyan biyu a rana.

Bayan haka wani direba Kingsley Chijindu dake daukan fansinjojoi daga Umuahia zuwa Aba ya koka da takuran da suke fama da shi a dalilin dokar.

Direbobin motocin haya sun bayyana cewa suna zabga asara mai yawa.