KORONA: Jihar Legas Ta Bude wuta, za ta yi wa mutane miliyan 4 rigakafi kafin Kirsimeti – Sanwo-Olu

Gwamnatin jihar Legas ta ce asibitoci masu zaman kansu za su rika karbar kudi daga masu zuwa yin rigakafin Korona, sai dai kuma kyauta za rika yi a asibitocin gwamnati.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya sanar da haka ranar Laraba a taron fara yi wa mutane allurar rigakafi a asibitocin masu zaman kansu a jihar.

Sanwo-Olu ya ce gwamnati ta hada hannu da asibitocin masu zaman kansu domin a yi wa mutum miliyan 4 rigakafin korona daga yanzu zuwa ranar 25 ga watan Disemba.

Yayin da hakan ke faruwa PREMIUM TIMES ta gano cewa babban asibitin zuciya da gwamnati ta gina dake Gbagadaa jihar na karban kudi kafin ta kula da mutanen da suka kamu da cutar korona.

Gidan jaridar ta gano cewa asibitin na karban naira 50,500 kudin gwajin korona sannan bayan sakamakon gwajin ya nuna mutum ya kamu da cutar kafin a kwantar da shi a asibitin sai an biya naira miliyan 1.35 wato kudin kwanaki hudu kenan.

Hakan na nufin cewa a rana mutum zai kashe naira 350,000 zuwa 400,000 kenan a rana kuma sai mutum yayi kwanaki 14 kwance kafin a sallameshi.

Kwamishinan yada labarai Gbenga Omotoso da mai taimakawa gwamnan Sanwo-Olu kan harkokin yada labarai Gboyega Akosile sun bayyana cewa asibitin gwamnati na karbar kudi saboda yadda attajiran jihar ke kin zuwa asibitin gwamnati a duba su duk da cewa asibitocin gwamnati na da kwararrun ma’aikata da kayan aiki na zamani fiye d wasu daga cikin asibitoci masu zaman kansu.

“Da dama daga cikin masu kudin jihar sun yi mana magana kan a kebe musu wani wuri da za a rika duba su wasu ma har cewa suke yi za su biya ko nawa ne. A dalilin haka ya ne yasa gwamnati ta saka farashi ga yin rigakafin.

“Yin haka zai taimaka wajen hana mutane zuwa baragurbin asibitoci masu zaman kansu.

Gwamna Sanwo-Olu ya ce gwamnatin sa a shirye take ta dauki matakan da za su taimaka wajen hana yaduwar korona musamman yanzu da ake gab da shiga watan Disemba.

Ya ce burin gwamnati shine yi wa akalla kashi 30% na mutanen jihar allurar rigakafin korona nan da shekara daya.

Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum miliyan 1.2 allurar rigakafin korona a jihar.

Sanwo-Olu ya ce daga ciki akwai mutum 550,000 da suka kammala yin allurar rigakafin a Legas.

Ya ce gwamnati da hukumar NPHCDA zasu hada hannu da asibitoci masu zaman kansu domin a kara yawan wuraren da ake yi wa mutane rigakafin Korona a jihar.

“Gwamnati na da burin ganin ta kara yawan wuraren da ake yi wa mutane allurar rigakafin zuwa 8,000 a fadin jihar.

Cutar korona

Zuwa yanzu mutum 77,723 ne suka kamu da cutar a jihar Legas daga cikin mutum 211,330 din da suka kamu a Najeriya.

Mutum 749 sun mutu a dalilin cutar sannan an sallami 76,926 a jihar Legas